Gwamnoni sun jinjinawa tsarin shugabancin Osinbajo, da yadda yake magance matsaloli

Gwamnoni sun jinjinawa tsarin shugabancin Osinbajo, da yadda yake magance matsaloli

- Gwamnoni sun yaba ma mataimakin Shugaban kasa Osinbajo a matsayin mutum mai tsarin jagoranci nagari a matsayinsa na Shugaban majalisar tattalin arziki na kasa

- Gwamnonin sun ce mataimakin Shugaban kasar ya dauki kowa a matsayi guda duk da banbancin jam’iyyun siyasarsu

- Sun amince da cewar majalisar tattalin arzikin ta sawwaka yadda ake kasuwanci a kasar saboda jajircewar Osinbajo

Gwamnoni sun bayyana mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a matsayin jagora nagari a matsayinsa na Shugaban majalisar tattalin arziki na kasa.

Osinbajo, wanda ya jagoranci taron NEC a ranar Alhamis, 24 ga watan Maris, ya yabi mambobin majalisar, wadanda suka hada da gwamnonin tarayya da gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) kan hadin kansu, jaridar Nation ta ruwaito.

Mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa sun jajirce wajen tabbatar da inganta tattalin arziki ba tare da la’akari da banbancin jam’iyyun siyasa ba.

Gwamnoni sun jinjinawa tsarin shugabancin Osinbajo, da yadda yake magance matsaloli

Gwamnoni sun jinjinawa tsarin shugabancin Osinbajo, da yadda yake magance matsaloli
Source: UGC

Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna, da sauran mambobin majalisar sun yabi mataimakin shugaban kasar bisa tawali’unsa da kuma yanayin jagorancinsa.

Abdulfatah Ahmed, gwamnan jihar Kwara, har ila yau ya bayyana cewa Osinbajo “ya jagoranci tawaga ta fannoni daban daban dake bukatan kulawa a tattalin arziki. Yayi kokari kwarai da gaske a fannin tsaro”.

Kashim Shettima, gwamnan jihar Borno yace mataimakin shugabn kasar ya baiwa kowa kula na musamman, yayin da Akinwunki Ambode na jihar Legas yace ya ba majalisar tunani na musamman.

KU KARANTA KUMA: Samar da tashar radiyon Fulani ya tabbatar da ikirarin Obasanjo – Kungiyar CAN

Udom Emmanuel, gwamnan jihar Akwa Ibom yace majalisar tattalin arzikin ta sawwaka yadda ake kasuwanci a kasar saboda jajircewar Osinbajo.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Osinbajo ya gargadi gwamnoni jihohi 36 na kasar da sauran mutane dake rike da mukaman jagoranci dasu kula da yanayin furucinsu don gudun rigingimun siyasa.

An rahoto cewa Osinbajo ya bayyana haka ne a ranar Alhamis, 23 ga watan Mayu a taron NEC wanda aka gudanar a fadar shugaban kasa, Abuja.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel