Yan Najeriya na fadin albarkacin bakinsu bisa hukunci kotun koli akan zaben Zamfara

Yan Najeriya na fadin albarkacin bakinsu bisa hukunci kotun koli akan zaben Zamfara

-Hukuncin da kotun koli ta yanke kan zaben jihar Zamfara na cigaba da samun tsokaci daga wurin mutanen Najeriya, wasu na matukar jin dadin hukuncin yayinda wasu ke jajantawa akan abinda ya faru.

Ana cigaba da samun cece kuce tsakanin jama’ar Najeriya yayin da kotun koli ta kasa ta yi fatali da Idris Koguna na jam’iyar APC a matsayin zababben gwamnan jihar Zamfara inda ta damka wa Bello Muhammad na jam’iyar PDP nasara.

Idan baku manta ba jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa hukuncin kotun kolin ya ayyana ilahirin kuri’un da jam’iyar APC ta samu a dukkanin zabukan jihar Zamfara a matsiyan “asarar kuri’a”, saboda haka duk yan takarar da suka kasance na biyu a mataki daban daban lokacin zaben suke da nasara a yanzu.

Yan Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu bisa hukunci kotun koli akan zaben Zamfara

Yan Najeriya sun tofa albarkacin bakinsu bisa hukunci kotun koli akan zaben Zamfara
Source: UGC

KU KARANTA:Tsuntsu daga sama gasasshe: Bello Mutawwalle na PDP zai zama gwamna a Zamfara

Tun da kotun koli ta fitar da wannan sanarwa, shafukan sadarwa suka cika makil da maganganun mutane, masu murna nayi, masu takaici da kuma wayyo Allah suna tayi.

Wani mutum mai suna Gidado da yake biye da hukuncin yayi magana a shafinsa na twitter kamar haka, “ Karshen alewa kasa, yau dai mun ga karshen girman kan Yari. Lokacin da muke ihun cewa jam’iyar APC bata gudanar da zaben fidda gwani ba a Zamfara babu irin sunan da ba’a kira mu da shi ba, to yau dai ga irinta nan.”

Kazalika, a shafin sadarwan na twitter Okolugbo yace, “ Hakika kotun koli ta bamu yanci sake gaskata shari’a. Su Yari kuma sai aje a sasanta da Oshiomole. Tabbas ina taya Zamfarawa murnar wannan hukunci na kotun koli.” Kamar yadda ya rubuta a shafin nasa.

Shi kuwa Aliyu cewa yayi, “ Daga kujerar gwamna, sanatoci da kuma yan majalisar wakilai hada da majalisar dokokin jihar Zamfara duk na PDP ne a yau, Allah da girma Yake.”

Yayin da muatne da dama ke sambarka da wannan hukunci, IsmaeelAhmedB ya nuna rashin jin dadinsa a shafinsa na twitter, “ Mun rasa jihohi guda biyu gabanin zabe, Zamfara da Ribas. Mun kuma rasa Adamawa da Imo saboda son kai.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel