Shegiyar Uwa: Hukumar Hisbah ta ceto yar jaririyar da mahaifiyarta ta birne da rai

Shegiyar Uwa: Hukumar Hisbah ta ceto yar jaririyar da mahaifiyarta ta birne da rai

Hukumar Hizbah, shiyar jihar Kebbi, ta ceto wata jaririyar yar kwanaki biyu da haihuwa bayan mahaifiyarta ta birneta da rai.

An gano gawar yar jaririyar kwana biyu bayan haihuwarta a bayan wani Otal dake cikin garin Birnin Kebbi.

Mahaifiyar yarinyar da wata kawarta sun kama daki a shahrarran Otal mai suna Zinari, na tsawon kwana biyu kuma suka silale suka birne yarinyar cikin dare a bayan Otal.

Diraktan bangaren Shari'a da harkokin addinin jihar, Alhaji Abubakar Muhammad Lamne Augie, ya ce kukan yar jaririyar ya jawo hankalin jama'a kuma suka cirota daga inda suka birneta.

KU KARANTA: Ikon Allah: Angulun da muka tsare ta ci N30,000 cikin kwanaki shida - Hukumar Yan sanda

Yace: "Mahaifyar yarinyar ta birne jaririyar da ranta bayan sun zauna a Zinari Hotel na tsawon kwana biyu."

Bayan birne jaririyar, sai suka leka ko yarinyar ta mutu. Amma da suka hakota, sai yarinyar ta fashe da kuka, sai suka ruga da gudu."

Ya ce yarinyar bata daina kuka ba har sai da jama'a suka ji kukan kuma suka ceceta. sai Jama'a cirota daga kasa, sannan suka sanar da hukuma domin ceton rayuwar yarinyar.

Kana mazauna unguwar sun shiga cikin Otal din kuma duka damke wadannan yan mata biyu.

Tsokaci: Hoton da muka sanya na bayani ne kawai, ba ainihin hoton jaririya bane.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel