Samar da tashar radiyon Fulani ya tabbatar da ikirarin Obasanjo – Kungiyar CAN

Samar da tashar radiyon Fulani ya tabbatar da ikirarin Obasanjo – Kungiyar CAN

Kungiyar Kiristocin Naajeriya (CAN) ta yi Allah wadai da yunkurin gwamnatin tarayya na samar da lasisin kafa tashar radiyo na Fulani tsantsa.

Fasto Bayo Oladeji, mataimaki na musamman ga Shugaban kungiyar Samson Ayokunle, yace yunkurin ya tabbatar da furucin da aka alakanta da tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo game da shirin mayar da kasar kan akidar Fulani da gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Muhammadu Buhari ke yi.

Yace: “An ruwaito a jaridu cewa gwamnatin tarayya na shirin bai wa kungiyar Miyetti Allah naira biliyan 100 gwamnati ta karyata hakan kawai sai gashi kungiyar Miyetti Allah ta furta cewa gwamnatin tsohon Shugaban kasa Goodluck Jonathan ce ta amince daa hakan. Wa ke yaudarar wani?

Samar da tashar radiyon Fulani ya tabbatar da ikirarin Obasanjo – Kungiyar CAN

Samar da tashar radiyon Fulani ya tabbatar da ikirarin Obasanjo – Kungiyar CAN
Source: UGC

“Me yasa ba a kafa wa makiyaya tashar radiyo ba suma? Ina tashar radiyon yan bindiga a Zamfara, ko na mayakan Niger Delta? Babu mutum ko guda da akaa hukunta akan kashe-kashe a arewa maso tsaakiya. Shin zargin tsohon Shugaban kasa Olusegun Obasanjo n cewaa ana shirin mayar da kasar kan akidar Fulani bai fara tabbata ba a yanzu?

KU KARANTA KUMA: Tsuntsu daga sama gasasshe: Bello Mutawwalle na PDP zai zama gwamna a Zamfara

“Duk wani balagagge a Arewa yana sauraron radiyo, toh mai zai sa ba za a isa ga makiyaya akan tashoshin radiyo da ke nan ba? Me yasa ake son kafa masu wani tashar radiyo na daban? Su daina yaudararmu.”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel