Zamfara: An ba hammata iska tsakanin magoya bayan APC da PDP a harabar kotun koli

Zamfara: An ba hammata iska tsakanin magoya bayan APC da PDP a harabar kotun koli

Wani bidiyo da ya billo a yanar gizo ya nuna yadda aka yi musayar naushi a tsakanin magoya bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Zamfara.

Lamarin dai ya afku ne a yau Juma’a, 24 ga watan Mayu a harabar kotun koli, yayinda ake zartar da hukunci akan zaben jihar.

Rikicin dai ya kaure ne bayan an yamutsa gashin baki tsakanin matasan jam’iyyun biyu.

Ga bidiyon a kasa:

Da farko dai Legit.ng ta rahoto cewa Kotun kolin Najeriya ta yanke hukuncin cewa jam'iyyar All Progressives Congress APC ba tada hakkin takara a zaben gwamnan jihar kuma saboda haka, an yi fatali da dukkan kuri'un da ta samu.

KU KARANTA KUMA: Tsuntsu daga sama gasasshe: Bello Mutawwalle na PDP zai zama gwamna a Zamfara

Gamayyar alkalai biyar na kotun sun yi ittifaki a ranar Juma'a cewa jam'iyyar APC bata gudanar da zaben fidda gwani ba bisa ga ka'idojin jam'iyyar.

Babban alkali, Paul Adamu Galinji, ya ce dukkan kuri'un da aka kadawa jam'iyyar APC banza ne kuma sannan jam'iyyar da tazo na biyu a zabubbukan ne zababbun masu kujerar.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel