Tsuntsu daga sama gasasshe: Bello Mutawwalle na PDP zai zama gwamna a Zamfara

Tsuntsu daga sama gasasshe: Bello Mutawwalle na PDP zai zama gwamna a Zamfara

Dan takarar gwmna na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben 2019, Dr Bello Muhammad Mutawalle na shirin zama gwmnan jihar bisa ga sakamakon da hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta saki a watan Maris.

Hukuncin kotun koli ta soke kuri’un APC a jihar sannan tayi umurnin cewa wanda ya samu kuri’u mafi yawa na biyu ya daura daga inda aka tsaya.

Don haka, sakamakon da hukumar INEC ta kaddamar ya nuna cewa Mutawalle na PDP ne zai karbi ragamar shugabanci a jihar kamar yadda shine ya zo na biyu bayan Mukhtar Shehu Idris na APC.

Tsuntsu daga sama gasasshe: Bello Mutawwalle na PDP zai zama gwamna a Zamfara

Tsuntsu daga sama gasasshe: Bello Mutawwalle na PDP zai zama gwamna a Zamfara
Source: Twitter

Baturen zaben gwamnan jihar, Farfesa Kabiru Bala yace Alhaji Mukhtar Shehu Idris ya samu kuri’u 534,541 yayinda abokin adawarsa na PDP Bello Muhammad Mutawalle ya smu kuri’u 189,452.

KU KARANTA KUMA: Jihar Plateau na daga cikin wadanda za su biya kudin hajji mafi karanci

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto cewa hukuncin kotun koli na soke kuri'un jam'iyyar APC a zaben gwamna na shekarar 2019 a jihar Zamfara ya sanya jama'a da dama murna a garin Gusau babban birnin Jihar Zamafara kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Masu babbura da dama suna ta yawa a titunan Gusau suna yabawa hukuncin kotun yayin da suke dauke da fostocin dan takarar gwamnan na jam'iyyar peoples Democratic Party ( PDP) Dr Bello Mutawalle Maradun.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel