'Yan bindiga sunyi garkuwa da mai shirya fina-finai, sun nemi N10m

'Yan bindiga sunyi garkuwa da mai shirya fina-finai, sun nemi N10m

Masu garkuwa da mutane sun sace wani fitaccen dan jarida kuma mai shirya fina-finai, Salisu Muazu a ranar Alhamis da yamma a hanyar Kaduna zuwa Jos.

A yayin da ya ke tabbatarwa kamfanin dillancin labarai, NAN afkuwar lamarin, dan uwansa, Sani Mua'azu wadda shima mai shirya fina-finai ne ya ce suna tafiya tare da wasu mutane biyu ne lokacin da abin ya faru.

'Yan bindiga sunyi garkuwa da mai shirya fina-finai, sun nemi N10m

'Yan bindiga sunyi garkuwa da mai shirya fina-finai, sun nemi N10m
Source: Facebook

"Mun hallarci wani taro a Kaduna kuma muna hanyarmu ta komawa Jos yayin da wasu 'yan bindiga suka tsare mu su kayi mana fashi a kauyen Jengre.

DUBA WANNAN: Akwai tartsatsin harsashi a idon Sheikh El-Zakzaky - ICRP

"Sunyi mana fashi amma na yi nasarar tserewa amma sun tafi da kani na Salisu da wasu mutane biyu da muka dako daga Kaduna.

"Sun kira mu a safiyar yau sun bukaci a biya su Naira 10,000,000 a matsayin kudin fansa kafin su sako su."

Mua'azu ya yi kira ga 'yan Najeriya su taya su da addu'o'i domin a sako dan uwansa da sauran mutanen biyu.

Sani da Salisu duk mazauna garin Jos ne kamar yadda NAN ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel