Kuma dai! Kotun koli ta tabbatar da nasarar gwamnan APC na jahar Ekiti

Kuma dai! Kotun koli ta tabbatar da nasarar gwamnan APC na jahar Ekiti

Kotun koli ta Najeriya tayi watsi da korafin da dan takarar jam’iyyar PDP a zaben gwamnan jahar Ekiti Kolapo Olusola Eleka ya shigar gabanta, inda ta tabbatar da nasarar Dakta Kayode Fayemi a matsayin zababben gwamnan jahar.

Kotun ta yanke wannan hukunci ne a ranar Juma’a, 24 ga watan Mayu jim kadan bayan hukuncin data yanke daya rushe dukkanin kuri’un da jam’iyyar APC ta samu a jahar Zamfara a zaben 2019, wanda hakan yasa APC ta rasa dukkanin kujerun data lashe a zaben.

KU KARANTA: Buhari ya nada Farfesa Hamidu a matsayin shugaban asbitin koyarwa na ABU dake shika

Kuma dai! Kotun koli ta tabbatar da nasarar gwamnan APC na jahar Ekiti

Fayemi
Source: Twitter

Legit.ng ta ruwaito Olusola Eleka ya daukaka kara zuwa kotun koli ne yana kalubalantar nasarar da Fayemi ya samu a zaben gwamnan jahar daya gudana a watan Yulin shekarar 2018, bayan kotun sauraron korafe korafe da kotun daukaka kara duk sun yi watsi da karar tasa.

Da suke yanke hukuncin, Alkalan kotun kolin su biyar a karkashin jagorancin Alkalin Alkalan Najeriya, Mai sharia Tanko Muhammad sun amince cewa dan takarar PDP bashi da wata hujjar shigar da wannan kara, don haka bashi da gaskiya.

INEC dai ta sanar da dan takarar APC Kayode Fayemi ya samu kuri’u 197,459, yayin da dan takarar jam’iyyar PDP, Olusola Eleka ya samu kuri’u 178,121 a zaben na ranar 14 ga watan Yulin 2018.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Online view pixel