Zargin juyin mulki: Atiku ya nemi a kama Lai Mohammed

Zargin juyin mulki: Atiku ya nemi a kama Lai Mohammed

- Dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, yayi kira ga a kama Lai Mohammed

- Atiku ya bayyana cewa ya zama dole a kama Mohammed kan zargin cewa yana shirin yiwa gwamnatin Buhari zagon kasa

- Tsohon mataimakin Shugaban kasar ya bayyana cewa furucin Mohammed ya kasance kokarin bata masa suna

Tsohon mataimakin Shugaban kasa kuma dan takarar Shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, yayi kira ga a kama ministan labarai, Alhaji Lai Mohammed cikin gaggawa saboda zargin yunkurin barazana ga tsaro.

Atiku ya ce Lai ya yi zargin cewa wasu na yunkurin shirya wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari zagon kasan juyin mulki, amma ya kasa gabatar da hujjojin haka din.

Har ila yau Atiku ya yi kira da Ministan ya rubuta masa takardar neman afuwa bisa kage da sharrin da ya yi masa.

Zargin juyin mulki: Atiku ya nemi a kama Lai Mohammed

Zargin juyin mulki: Atiku ya nemi a kama Lai Mohammed
Source: Depositphotos

Dan takarar ya bayyana cewa furucin Mohammed ya kasance kokarin bata masa suna.

Ya ce yin hakan zai sa Lai ba za ya sake yin irin wannan kasassabar magana ba, wadda ke da barazana ga tsaron kasa.

Atiku ya ragargaji gwamnatin Buhari da yin sakaci da kuma rashin iya aiki, ta yadda har Buhari ya kasa gargadin Lai dangane da irin sakin-bakin da ya ke yi, wanda Atiku ya ce barazana ne ga tsaron kasar nan.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: An zabi gwamnan Kebbi a matsayin shugaban kungiyar gwamnonin APC

Atiku ya ce har yanzu wasu baragurbi kuma dibgaggu na nan su na kitsa makarkashiya da sharri a kasar nan, a karshe domin su goga masa bakin fenti kuma su bata masa suna.

Daga karshe ya yi kira ga gwamnati ta maida hankali wajen tabbatar da tsaron al’ummar kasar nan, maimakon ta yi tsaye zororo ta bar manyan jami’an ta sun bar jaki su na dukan taiki.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel