Zamfara ta cika da murna bayan hukuncin kotun koli a kan APC

Zamfara ta cika da murna bayan hukuncin kotun koli a kan APC

Hukuncin kotun koli na soke kuri'un jam'iyyar APC a zaben gwamna na shekarar 2019 a jihar Zamfara ya sanya jama'a da dama murna a garin Gusau babban birnin Jihar Zamafara kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Masu babbura da dama suna ta yawa a titunan Gusau suna yabawa hukuncin kotun yayin da suke dauke da fostocin dan takarar gwamnan na jam'iyyar peoples Democratic Party ( PDP) Dr Bello Mutawalle Maradun.

Zamfara ta cika da murna bayan hukuncin kotun koli a kan APC

Zamfara ta cika da murna bayan hukuncin kotun koli a kan APC
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Akwai tartsatsin harsashi a idon Sheikh El-Zakzaky - ICRP

Mazauna garin Gusau kuma sun bayyana mabanbanta ra'ayoyi game da hukuncin babban kotun inda wasu da yawa cikinsu su kayi fatan alheri ga gwamnatin da za ta kama aiki nan ba da dadewa ba.

"Ina fatan sabuwar gwamnatin za ta inganta rayuwar mutane. Banyi mamakin hukuncin kotun ba duba da abubuwan da suka rika faruwa tun daga lokacin da aka fara zabukkan cikin gida zuwa yanzu," inji wani magidancin mai suna Aliyu Hussain.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel