Yanzu Yanzu: An zabi gwamnan Kebbi a matsayin shugaban kungiyar gwamnonin APC

Yanzu Yanzu: An zabi gwamnan Kebbi a matsayin shugaban kungiyar gwamnonin APC

- Kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC ta zabi Gwamna Bagudu na jihar Kebbi a matsayin shugabanta

- Gwamna Fayemi yayi nasara a zaben shugabancin kungiyar gwamnonin Najeriya

- Bagudu zai maye gurbin gwamnan Jihar Imo mai barin gado, Rochas Okorocha

An zabi gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu, a matsayin shugaban Kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC

Legit.ng ta rahoto cewa kungiyar ta bayyana haka ne a shafinta na tweeter a ranar Juma’a, 24 ga watan Mayu.

An tattaro cewa an zabi Bagudu ne a taron gwamnoni da aka gudanar a Abuja a daren ranar Alhamis, 23 ga watan Mayu, a masaukin gwamna.

Bagudu, wanda aka hada kai aka zabe shi, zai maye gurbin Gwamnan jihar Imo, Rochas Okorocha wanda mulkinsa zai kare a ranar 29 ga watan Mayu.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa an zabi Gwamna Kayode Fayemi, wanda ya kasance tsohon ministan albarkatun kasa a matsayin shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya a lokacin taron kungiyar a Abuja.

KU KARANTA KUMA: Zango na biyu: Shugaba Buhari zai yi sallar Juma’a a babban masallacin kasa a yau

An rahoto cewa gwamnan jihar Ekiti ya yi nasara a matsayin wanda aka fi so ya gudanar da harkokin kungiyar bayan gwamnonin sun ki amincewa da gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel