Jihar Plateau na daga cikin wadanda za su biya kudin hajji mafi karanci

Jihar Plateau na daga cikin wadanda za su biya kudin hajji mafi karanci

Hukumar kula da jigilar alhazai ta jihar Plateau tace kudin mahajjantan ta na 2019 ya kai naira 1,519,513 wanda ya kasance mafi karancin farashi a jihohin Arewa 19 baya ga jihar Adamawa wanda ya kasance kasa da haka.

Babban Sakataren hukumar, Auwal Abdullahi, ya bayyana hakan a jawabin da ya gabatar a jiya Alhamis, 23 ga watan Mayu.

Ya bukaci mahajjata wadanda suka soma biyan wani bangare na kudin hajjin 2019 dasu cika kudin; wadanda kuma basu biya ba su gaggauta biya kafin kammalar shirin a farkon makon watan Yuni.

Jihar Plateau na daga cikin wadanda za su biya kudin hajji mafi karanci

Jihar Plateau na daga cikin wadanda za su biya kudin hajji mafi karanci
Source: Depositphotos

A wani lamari makamancin haka, Legit.ng ta rahoto cewa hukumar kula da aikin Hajji ta jihar Adamawa ta bayyana adadin kudin da za a biya a shekarar nan domin sauke farali a kasa mai tsarki.

Hukumar da ke kula da harkokin aikin Hajjin da jin dadin Alhazai na Adamawa ta bayyana cewa Mahajjatan da za su tashi ta jihar Adamawa, za su kashe Naira miliyan 1, 510, 000 ne a shekarar bana.

KU KARANTA KUMA: Zango na biyu: Shugaba Buhari zai yi sallar Juma’a a babban masallacin kasa a yau

Babban Sakataren wannan hukuma, Malam Umar Bobboyi, shi ne ya bayyana wannan a Ranar Lahadi 19 ga Watan Mayun 2019. Bobboyi yayi wannan jawabi ne a cikin babban birnin Adamawa na Yola.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel