Buhari ya nada Farfesa Hamidu a matsayin shugaban asbitin koyarwa na ABU dake shika

Buhari ya nada Farfesa Hamidu a matsayin shugaban asbitin koyarwa na ABU dake shika

Gwamnatin tarayya ta nada Farfesa Ahmed Hamidu a matsayin babban likita kuma sabon shugaban asibitin koyarwa ta jami’ar Ahmadu Bello dake garin Shika, cikin garin Zaria na jahar Kaduna.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito sanarwar ta fito ne daga bakin kaakakin ma’aikatar kiwon lafiya, Boade Akinola inda yace sabon shugaban zai yi wa’adin shekaru hudu ne daga ranar 14 ga watan Mayun shekarar 2019.

KU KARANTA: Za’a koma gidan jiya: Malaman jami’a zasu koma yajin aikin ‘sai baba ta ji’

Buhari ya nada Farfesa Hamidu a matsayin shugaban asbitin koyarwa na ABU dake shika

Buhari ya nada Farfesa Hamidu a matsayin shugaban asbitin koyarwa na ABU dake shika
Source: UGC

Da yake taya Hamidu murna, ministan lafiya na Najeriya, Farfesa Isaac Adewale ya jaddada masa manufar gwamnatin tarayya na inganta kiwon lafiya a Najeriya, tare da tuna masa nauyin dake rataye a wuyansa na tafiyar da babbar cibiyar kiwon lafiya ta shika.

Don haka Minista Adewole ya yi kira ga sabon shugaban ya daura akan nasarorin da tsohon shugaban Asibitin ya samar don tabbatar da amincewar da shugaban kasa keda shi akansa.

An haifi Hamidu ne a ranar 24 ga watan Nuwambar 1950 a garin Bunza dake jahar Kebbi, inda ya halarci makarantar Firamari ta Nassarawa Primari School data Mekrar Gandu a Birnin Kebbi, sa’annan yayi karatun sakandari a makarantar gwamnati ta Nagarta college Sakkwato da FGC Warri.

Daga nan ya wuce jami’ar jahar Kharkov ta kasar Ukraine a shekarar 1971 -72, jami’ar kiwon lafiya ta Kiev dake Ukraine daga 1972-78, sai ya dawo jami’ar ABU bangaren kula da yara daga 1981 – 1989, sai ya wuce jami’ar Liverpool don kara karatu daga 1986 – 1988.

Daga karshe Farfesa Ahmed Hamidu yana da mata daya da yara bakwai, daga cikin yaran akwai likitoci biyu mata, kwararren mai hada magunguna kuma malamin jami’a, Soja, dalibar liktanci, dalibin jami’a guda daya da kuma na karshen dalibin sakandari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel