Yanzu Yanzu: Firaministar Birtaniya Theresa May ta yi murabus

Yanzu Yanzu: Firaministar Birtaniya Theresa May ta yi murabus

- Firaministar kasar Birtaniya Theresa May ta sanar da murabus dinta bayan ta gaza gabatar da yarjejeniyar Brexit

- May ta bayyana cewa tayi iya bakin kokarinta sannan tana fatan wanda zai gaje ta zai yi nasara a inda ta gaza

- Cikin kuka tace ita ce mace ta biyu da ta riki mukamin Firaminista amma ba ita zata zamo ta karshe ba

Firaministar kasar Birtaniya Theresa May ta sanar da murabus dinta bayan ta gaza gabatar da yarjejeniyar Brexit, inda ta kara da cewa tayi iya bakin kokarinta sannan tana fatan wanda zai gaje ta zai yi nasara a inda ta gaza.

Tayi sanarwar ne a Unguwar Downing a ranar Juma’a, 24 ga watan Mayu, inda tayi amfani da damar wajen jero nasarorin da ta samu, shafin BBC ta ruwaito.

Yanzu Yanzu: Firaministar Birtaniya Theresa May ta yi murabus

Yanzu Yanzu: Firaministar Birtaniya Theresa May ta yi murabus
Source: UGC

Cikin kuka mai taba zuciya, tace ita ce mace ta biyu da ta riki mukamin Firaminista amma ba ita zata zamo ta karshe ba.

KU KARANTA KUMA: Zango na biyu: Shugaba Buhari zai yi sallar Juma’a a babban masallacin kasa a yau

Hakan na zuwa ne a dai dai lokacin da al'ummar kasar ke kada kuri'a a zaben Majalisar Tarayyar Turai kuma wani hasashe ke nuna cewa bangaren masu ra'ayin ci gaba da zaman Birtaniyar a EU zai samu gagarumin rinjaye.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel