Kafa sabbin masarautu wani shiri ne na almubazaranci da baitulmalin Kano - Abba Gida Gida

Kafa sabbin masarautu wani shiri ne na almubazaranci da baitulmalin Kano - Abba Gida Gida

Dan takaran gwamna a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Kano a zaben da ya gabata, Abba Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida Gida, a jiya Alhamis, 23 ga watan Mayu ya bayyana sabbin masarautu da aka kafa a matsayin shiri na makiyan jihar don ganin sun kashe dukiyar al’umma.

Yayin da yake magana bayan bude baki tare da mambobin kungiyoyi daban-daban a sashin sufuri, Yusuf ya zargi Gwamna Abdullahi Ganduje da daukaka ayyukan da ba zasu amfani al’umma ba ta hanyar kafa sabbin masarautu, tsige sakatarori na dindindin tare da zargin manyan malamai a jihar.

Yace: “A lokacin da babban damuwar mu a jihar Kano ya kasance inganta kayayyakin more rayuwa kamar makarantu da asibitoci don samar da cigaba, makiyan jihar suna yunkurin banzatar da dukiyar al’umma.

Kafa sabbin masarautu wani shiri ne na almubazaranci da baitulmalin Kano - Abba Gida Gida

Kafa sabbin masarautu wani shiri ne na almubazaranci da baitulmalin Kano - Abba Gida Gida
Source: Twitter

“Mun fahimci cewa Gwamna Ganduje na shirin kashe daruruwan miliyoyi wajen gine-ginen fadar masarautu da siyan motocin sarakuna ga sabbin sarakuna wanda hakan zai shafi rayukan al’umma wadanda basu iya biyan ko kudin makarantan yaransu.

KU KARANTA KUMA: Gwamna Masari ya soke bikin ranar 29 ga watan Mayu

"Muna son mu ja hankulan gwamna cewa ba wadannan ayyukan bane a gabanmu a jiha mai dauke da al’umma fiye da miliyan uku wadanda suka bar makaranta, akalla matasa miliyan hudu marasa aiki da miliyoyin almajirai a tituna saboda rashin mu’halli”.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Online view pixel