'Yan bindiga sun yiwa 'dan kasuwa yankan rago a Ribas

'Yan bindiga sun yiwa 'dan kasuwa yankan rago a Ribas

A daren ranar Larabar da ta gabata bayan kashe wani dan kasuwa mai sunan Chima a birnin Fatakwal na jihar Ribas, 'yan bindiga sun kuma yanke kansa kamar yadda jaridar The Punch ta ruwaito.

Bayan kashe Chima ta hanyar harbi da harsashi na bindiga, masu ta'adar sun kuma yanke kan sa a gaban iyalin sa cikin yankin gundumar Rumuekini dake karamar hukumar Obior-Akpo ta jihar Ribas.

'Yan bindiga sun yiwa 'dan kasuwa yankan rago a Ribas

'Yan bindiga sun yiwa 'dan kasuwa yankan rago a Ribas
Source: UGC

Wani mashaidin wannan mugun ji da mugun gani da ya bukaci a sakaya sunan sa ya bayyana cewa, yayin da lamarin ya auku da misalin karfe 11.00 na daren Laraba, 'yan ta'adda sun yi amfani da dabarar kashe janareton marigayi Chima domin samun damar tilasta mas sa fitowa waje.

Yayin tuntuba ta manema labarai, kakakin hukumar 'yan sanda na jihar Ribas, Nnamdi Omoni ya tabbatar da aukuwar wannan ta'addanci tare da shan alwashin bankado miyagun da suka aika shi.

KARANTA KUMA: Buhari ya kaddamar da sabon filin jirgin sama a jihar Imo

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, kisan Chima ya auku duk da gargadin gwamnatin jihar da kuma Sarakunan gargajiya akan tashi tsaye wajen kawo karshen aukuwar ta'addanci na zubar jini da salwatar rayukan al'umma a jihar.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel