Babachir ya shiga tsaka mai wuya yayin da EFCC ta gabatar da wani kwakkwaran shaida

Babachir ya shiga tsaka mai wuya yayin da EFCC ta gabatar da wani kwakkwaran shaida

Hukumar yaki da rashawa da yi ma tattalin arzikin kasa zagon kasa, EFCC, ta gabatar ma babbar kotun tarayya dake zamanta a Maitama Abuja da wani shaida a karar data shigar da tsohon sakataren gwamnati kuma na hannun daman shugaban kasa Muhammadu Buhari, Babachir David Lawal.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito EFCC ta gurfanar da Babachir, Hamidu David, Suleiman Abubakar da Apeh John Monday da kamfanoni guda biyu; Rholavision Engineering Ltd da Josmon Technologies Ltd a gaban Alkali Jude Okeke kan tuhumarsu da aikata laifuka 10 daya danganci satar naira miliyan 500.

KU KARANTA: Matsalar tsaro: Tawagar manyan hafsoshin Soja da Yansanda sun sauka jahar Katsina

A zaman farko na sauraron karar EFCC ta gabatar ma kotu da Malam Hamza Adamu Buwai, wanda ma’aikaci ne a ma’aikatar masana’antu, kasuwanci da zuba jari, kuma shine jami’I mai kula da kudi na kwamitin shugaban kasa mai kula da Arewa maso gabas, PINE.

Hamza ya shaida ma kotu cewa shine yake kula da biyan kudaden duk yan kwangilar da suka yi ma PINE aiki, albashin kwararru da kwamitin ta dauka haya da kuma albashin ma’aikatanta, don haka yace shine ya biya kamfanin Rholavision kudin aikin da tayi.

Hamza yace kamfanin ta gudanar da bada shawara irin na kwararru akan aikin cire ciyayi a tafkin Kamadugu dake jahar Yobe tare da gina kofofin ruwa na tsawon kilomita 250, aikin da aka baiwa kamfan Josmon Technologies.

Shaidan na EFCC ya kara da cewa ya san lokacin da Rholavision ta kai Josmon zuwa inda za’a gudanar da aikin, kuma suka fara aiki, har zuwa lokacin da suka kusan kammala aikin inda Rholavision ta mika masa takardar kammala kashi 95 na aikin don ya biyasu.

Yace da wannan ya bada umarnin a biya Josmon naira miliyan 258, daga cikin kudin kwangilar naira miliyan 272, bayan sun cika dukkanin sharuddan samun kudinsu, tare da bin dukkanin ka’idojin biyan kudin, amma saboda karancin kudi naira miliyan 225 aka iya biyansu. Haka gwamnati ta biya Rhola naira miliyan 3.5, kashi 50 na kudin aikinta.

Sai dai lauyoyin masu kara da wanda ake kara sun yi ta kai ruwa rana a gaban kotu akan sahihanci ko akasin haka na takardun biyan kudin da gwamnati tayi ma kamfanonin biyu, wanda hakan yasa Alkalin kotun ya dage yanke hukunci akan batun zuwa ranar 17 da 18 ga watan Yuni.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel