Gwamnatin tarayya na yiwa gwamnoni jihohi halacci, inji Buhari

Gwamnatin tarayya na yiwa gwamnoni jihohi halacci, inji Buhari

-Gwamnatin tarayya tayi alkawarin zata cigaba da taimakon gwamnoni kamar yadda ta saba, shugaba Buhari wanda mataimakinsa ya wakilta a jihar Imo domin kaddamar da wasu muhimman ayyukan da Okorocha yayi shine ya fadi wannan kalami.

Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Alhamis ya fadi cewa gwamnatin tarayya na kyautatawa gwamnonin jihohi.

Buhari wanda ya fadi wannan magana a Oweri babban birnin jihar Imo jim kadan bayan ya kammala kaddamar da wasu muhimman ayyuka da gwamna mai mubarus na jihar Imo, Rochas Okorocha ya aiwatar, yace gwamnatinsa na baiwa gwamnoni taimako kwarai da gaske.

Gwamnatin tarayya na yiwa gwamnoni jihohi halacci, inji Buhari

Gwamnatin tarayya na yiwa gwamnoni jihohi halacci, inji Buhari
Source: UGC

KU KARANTA:EFCC ta maka wani dan kasuwa kotu akan badakkalar N115m

Yace gwamnoni masu amana na iya kula da al’amuran jiharsu ba tare da neman wani taimako daga wurin gwamnatin tarayya ba.

Daga cikin ayyukan da shugaban ya kaddamar a jihar akwai tashar jirgin sama ta Sam Mbakwe, sabuwar shelkwatar ‘yan sanda da kuma asibitin iyaye mata da kananan yara duk a Owerri babban birnin jihar Imo.

Shugaban wanda mataimakinsa Yemi Osinbajo ya wakilta yace, gwamnoni na da bukatar su kasance masu zurfin tunani domin ciyar da jihohinsu gaba.

Da yake jinjinama Okorocha, shugaban yace, “ Gwamnatin tarayya da jam’iyar APC na alfahari da kai. Da irin wannan cigaban da ka kawo ma jiharka, hakan zai iya samuwa daga wurin sauran gwamnoni ba tare da sun nemi taimakon gwamnatin tarayya ba.”

“ Gwamnatin tarayya ta kasance mai taimakon gwamnonin jihohi. Kuma zamu cigaba da yin hakan kamar yadda muka saba.”

Okorocha wanda yayi magana a wurin cewa yayi, garkame asusun jihar da hukumar EFCC tayi na tsawon wata uku sam bai masu dadi ba.

Wannan abu ya dakatar da ayyukan gwamnatin jihar tasu da dama. Gwamnan yace, “ Wannan kadan ne daga cikin ayyukan da mukayi amma gashi kuma EFCC ta garkame asusunmu tsawon wata uku kenan yanzu, kari akan hakan kuma an hani ni shahadar lashe zabe.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel