Matsalar tsaro: Tawagar manyan hafsoshin Soja da Yansanda sun sauka jahar Katsina

Matsalar tsaro: Tawagar manyan hafsoshin Soja da Yansanda sun sauka jahar Katsina

Wasu manya manyan zababbun hafsoshi hukumomin tsaro na Najeriya sun dira jahar Katsina a ranar Alhamis, 23 ga watan Mayu a kokarinsu na bincike tare da samun bayanai game da barnar da yan bindiga suka aikata a wasu kananan hukumomin jahar.

Wannan tawaga ta isa jahar Katsina ne bisa umarnin shugaban kasa kuma babban kwamandan hafsoshin tsaro na Najeriya, Muhammadu Buhari, wanda ya umarci babban sufetan Yansanda Adamu Muhammed da shugaban hafsoshin Sojan Najeriya, Janar Abayomi O. dasu tafi Katsina don samo masa bayanai.

KU KARANTA: Yan gudun hijira na cikin tashin hankali saboda yunwa, 8 sun mutu

Bugu da kari Legit.ng ta ruwaito a ranar Laraba ma sai da shugaba Buhari ya gayyaci gwamnan jahar Katsina, Aminu Bello Masari zuwa fadar shugaban kasa domin su tattauna game da matsalar tsaro a Katsina, inda suka kwashe awanni har cikin dare suna ganawa.

Don haka koda tawagar manyan jami’an Soji da Yansanda ta isa Katsina sai dai suka yi arba da mataimakin gwamna Mannir Yakubu da sakataren gwamnati Mustapha Inuwa, a karkashin jagorancin Manjo janar B.I Ahanotu.

Sauran yan tawagar sun hada da mataimakin sufetan Yansanda Abdulmajid Ali, kwamandan Birget ta 17 dake Katsina, Birgediya L Omoniyi, da wasu manyan hafsoshi daga rundunar sojan kasa, ta sama, Yansanda da kuma hukumar tsaro ta farin kaya.

Sai dai tawagar bata bayyana ma manema labaru iya kwanakin da zata yi a jahar tana gudanar da wannan bincike kamar yadda shugaban kasa Buhari ya umarta ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel