Daukan dala ba gammo: An kama mutane 140 da suka shirya yi ma Buharu juyin mulki

Daukan dala ba gammo: An kama mutane 140 da suka shirya yi ma Buharu juyin mulki

Wata kotun majistri dake zamanta a garin Enugu a karkashin jagorancin Alkali mai sharia A.N Chioke ta bada umarnin garkame wasu tsagerun yayn kungiyar rajin kafa kasar Biyafara ta IPOB bisa tuhumar da Yansanda suke musu na shirya yi ma shugaban kasa Buhari juyin mulki.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar Alhamis, 23 ga watan Mayu ne Yansanda suka taso keyar tsagerun a cikin motocin bas bas kirar 608 da kuma wata mai cin mutane 18 zuwa kotun, inda ake tuhumarsu da aikata laifin cin amanar kasa.

KU KARANTA: Yan gudun hijira na cikin tashin hankali saboda yunwa, 8 sun mutu

Sai dai saboda tsananin yawansu hakan yasa a farfajiyar kotun aka gudanar da zaman shari’ar tasu domin kuwa dakin kotun ba zai daukesu ba, Dansanda mai shigar da kara ya bayyana cewa laifin da tsagerun suka aikata ya saba ma sashi na 516 (A) na kundin dokokin Najeriya.

Amma da aka karanta musu tuhume tuhumen da ake musu, sai dukkansu 140 suka musanta aikata laifina, hakan tasa guda daga cikin lauyoyin dake karesu, Osita Abalu ya nemi kotu ta bada belinsu, tun babu wata hujja akansu, a cewarsa.

Shima guda daga cikin lauyoyinsu, F.C Okeke ya bayyana cewa abin dariya ne ace wai yayan IPOB suna shirin hambarar da gwamnatin Buhari, saboda a cewarsa an kamasu ne yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa jana’iza.

Bayan sauraron dukkanin bangarorin biyu, Alkali Chioke ya bayyana cewa bashi da hurumin sauraron karar, don haka ya bada umarnin a garkamesu a gidan yarin Enugu har sai masu kara sun shigar dasu kara a kotun data dace.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel