Kalaman Buhari ‘ba su dace da ministocinsa ba’

Kalaman Buhari ‘ba su dace da ministocinsa ba’

-Wani mai fashin baki kan lamuran yau da kullum a Najeriya ya yi korafi akan kalaman yabo da shugaba Buhari yayi wa ministocinsa inda yake ganin da dama daga cikinsu basu cancanci yabawa ba.

Jawabin Shugaba Buhari a taron majalisar ministocinsa ya janyo cece kuce, bayan ya yaba da aikin ministocin tare da kin sauke su kafin cikar wa’adinsa na farko.

A ranar Laraba ne majalisar zartarwa ta Najeriya ta yi zaman bankwana kafin karewar wa’adin mulkin Shugaba Buhari na farko.

Kalaman Buhari ‘ba su dace da ministocinsa ba’

Kalaman Buhari ‘ba su dace da ministocinsa ba’
Source: Twitter

KU KARANTA:Kashe kashen Binuwe: BMO surutu kawai ta iya, inji Dakta Wayas

A yayin da yake jawabi, Shugaba Buhari yace irin rawar da ministocin suka taka ne dalilin da ya sa ya cigaba da tafiya da su har tsawon shekaru uku da rabi ba tare da ya sauya su ba.

Shugaban ya dada cewa, ministocin za su cigaba da rike mukamansu har sai nan da kwana bakwai masu zuwa wato ranar da wa’adinsa na farko zai kare.

Sai dai kuma wannan batu baiwa mutane da dama dadi ba, inda wasu ke ganin cewa jawabin shugaban ya nuna alamun zai iya cigaba da aiki da yawancin ministocin duk da cewa ba wata rawar azo a gani su kayi ba.

Dakta Abubakar Kari, mai sharhi kan lamuran yau da kullum a Najeriya ya shaidawa BBC cewa “ babu shakka shugaban zai bar wasu ko ma ya bar da dama daga cikin ministocin.”

“ Idan har kana tare da mutum ka cigaba da yaba mashi, to ba mamaki cigaba da tafiya da shi kake son yi.” Inji Kari.

Ya kara da cewa, tun tuni yakamata a ce shugaban ya canza ministocinsa saboda “ babu wata rawa da suka taka wurin kawo ma kasa cigaba.”

Dakta Kari ya bayyana cewa akwai ministocinsa da basu yi abin azo a gani ba, idan har shugaban zai cigaba da aiki tare da wasu cikinsu, “to su ba su cancanta ba.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit Newspaper

Tags:
Mailfire view pixel