Akwai tartsatsin harsashi a idon Sheikh El-Zakzaky - ICRP

Akwai tartsatsin harsashi a idon Sheikh El-Zakzaky - ICRP

Wata kungiya mai suna Initiative for Conciliation and Right Protection, ICRP, a ranar Alhamis 23 ga watan Mayu ta yabawa gwamnatin tarayya saboda bawa likitoci daga kasashen ketare damar duba shugaban IMN, Sheikh Ibrahim El Zakzaky da matarsa.

Kungiyar ta bukaci gwamnati ta kyalle El-Zakzaky da matsarsa su tafi kasar waje domin likitoci su duba su ta ce "akwai tartsatsin harsashi a idonsa na gefen hagu."

ICRP karkashin jagorancin Geoffrey Netochukwu, Godwin Ekoja, Bala Hassan, Ahmad Isa da Adelaja Adeoye ta ce duk da cewa gwamnati ta bawa El-Zakzaky da matarsa daman ganin likitoci, rahatonni sun nuna cewa akwai bukatar su tafi kasar waje domin jinya kamar yadda ya ke cikin sanarwar da Ahmad Isa ya karanta.

Akwai tartsatsin harsashi a idon Sheikh El-Zakzaky - ICRP

Akwai tartsatsin harsashi a idon Sheikh El-Zakzaky - ICRP
Source: Twitter

DUBA WANNAN: An sake rufe wani gidan shakatawa a jihar Kano saboda ayyukan masha'a

Ya ce, "Bincike ya nuna cewa El Zakzaky da matarsa na bukatar kulawa na musamman har ma da tiyata wadda ba za a iya yi a Najeriya ba.

"Abin alfahari ne ganin cewa gwamnati tayi biyaya ga umurnin kotu na barin El Zakzaky da matsara su ga likitocin da su ke ra'ayi bayan shekaru hudu da tsare shi.

"Muna bakin cikin yadda ake cigaba da tsare Sheikh da matarsa yayin da lafiyarsu ke kara tabarbarewa duk da umurnin da kotun tarayya karkashin Jastis Gabriel Kolawole ta bayar a 2016 na sakin sa."

Ya kara da cewa, "Muna kira ga gwamnatin tarayya karkashin shugaba Muhammadu Buhari ta bawa Sheikh Zakzaky da matarsa damar fita kasar waje domin yi musu magani sakamakon raunin da suka samu a hannun sojoji.

"Kwararrun likitocin da suka zo Najeriya suka duba shi sun ce yana bukatar da tafi da shi kasar waje domin yi masa magani musamman idon sa na hagu da ke dauke da tartatsin harsashi. Ya kamata gwamnati da dauki lamarin da muhimmanci."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel