NNPC ya bayyana ranar da mutanen da ya zaba don daukar aiki zasu rubuta jarrabawa

NNPC ya bayyana ranar da mutanen da ya zaba don daukar aiki zasu rubuta jarrabawa

- Kamfanin man fetur na kasa (NNPC) ya bayyana ranar 1 ga watan Yuni a matsayin ranar rubuta jarrabawa ta kwamfuta mai kwakwalwa ga mutanen da ya zaba domin dauka aiki

- Kamfanin ya ce za su cigaba da tantance mutanen domin fitar da wadanda ba su cancanta ba

Kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) ya bayyana cewa mutanen da ya zaba domin dauka aiki zasu yi jarrabar na'ura mai kwakwalwa wato (Computer Based Testing) a turance ranar Asabar 1 ga watan Yuni, 2019 a fadin kasar nan.

Mista Ndu Ughamadu, mai magana da yawun kamfanin shine ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis a Abuja.

Ya ce jarrabawar da mutanen za su yi ita ce zagaye na uku na hanyar daukar aikin.

NNPC ya bayyana ranar da mutanen da ya zaba don daukar aiki zasu rubuta jarrabawa

NNPC ya bayyana ranar da mutanen da ya zaba don daukar aiki zasu rubuta jarrabawa
Source: UGC

Ughamadu ya bayyana cewa za a gabatar da jarrabawar a cibiyoyi kusan guda 50 a fadin kasar nan, inda ya ce wadanda suka samu nasarar haye jarrabawar za a kira su a zagaye na karshe domin yin hira dasu baki da baki.

"An tura wa mutanen da aka zaba din sakonnin ta wayoyinsu akan yadda jarrabawar za ta kasance, yayin da za a turawa kowa gurin da zai yi jarrabawar da lokacin yin jarrabawar kafin ranar 27 ga watan Mayun nan," in ji shi.

KU KARANTA: Bayan shafe shekaru 8 yana mulki, Al-Makura yana rokon zababben gwamna akan ya kara masa wa'adin wata 3

Ughamadu ya ce za su cigaba da tantance mutane ta hanyar takardunsu, saboda haka duk mutumin da aka ga ya bayar da takardun karya za a kore shi daga cikin jerin mutanen da za a dauka aikin.

Idan ba a mance ba kwanakin baya kamfanin ya fitar da sanarwar cewar zai dauki ma'aikata aiki a fadin kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit.ng News

Mailfire view pixel