Buhari ya kaddamar da sabon filin jirgin sama a jihar Imo

Buhari ya kaddamar da sabon filin jirgin sama a jihar Imo

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da katafaren filin jirgin saman kasa da kasa na Sam Mbwake da gwamnatin jihar Imo ta kammala a karkashin jagorancin gwamna Rochas Okorocha.

Shugaban kasar cikin sanya aminci da kuma bayyana farin cikin sa, ya yaba da nagarta gami da ingancin babban aikin na ci gaba da a cewar sa ya kasance jigo na abun alfahari ga kasa baki daya.

Buhari tare da gwamnan jihar Imo; Rochas Okorocha

Buhari tare da gwamnan jihar Imo; Rochas Okorocha
Source: Facebook

Shugaban kasa Buhari wanda mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo ya wakilta yayin kaddamar da aiki ya bayyana cewa, filin jirgin saman kasa da kasa na Sam Mbakwa ba zai kasance cibiyar hada hadar kasuwanci kadai ba ga al'ummar jihar Imo.

Ya ce katafaren jirgin saman da aka assassa da manufa ta shige da ficen kayayyaki wato Cargo, zai bunkasa hanyoyin samar da ayyukan yi gami da inganta jin dadin rayuwar al'ummar jihar Imo da kuma na kasa baki daya.

A yayin da samar da ayyukan yi ya kasance daya daga cikin manyan akidu da kuma tsare-tsaren gwamnatin Buhari, Farfesa Osinbajo ya yaba da kwazon gwamna Rochas tare da kwadaitar da sauran jihohi wajen koyi da wannan abun alfahari.

KARANTA KUMA: Jihohi 14 sun ki amincewa da shirin kula da lafiyar al'ummar su

Baya ga katafaren aikin na tashar saukar kayayyaki a filin jirgin sama na Sam Mbakwe, mataimakin shugaban kasa ya kuma kaddamar da wasu ayyukan ci gaba da suka hadar da ginin sabuwar hedikwatar hukumar 'yan sanda da kuma ta hukumar gidajen yari.

Sauran ayyukan da mataimakin shugaban kasa ya kaddamar a madadin shugaban kasa Buhari sun hadar da asibitin Mata da kuma kananan Yara, sabuwar hanyar da aka yiwa lakani da Titin Gidauniyar Rochas, asibitin Somto da kuma sauran ayyuka na ci gaba.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel