Ta fara bayyana: Sunan daya daga cikin ministocin da ba zasu dawo ba ya bayyana

Ta fara bayyana: Sunan daya daga cikin ministocin da ba zasu dawo ba ya bayyana

Ministan sadarwa, Adebayo Shittu, ba zai samu dawowa cikin majalisar ministocin shugaba Muhammadu Buhari ba a wa'adinsa na biyu, majiyarmu ta tabbatar.

Majiya mai karfi ta bayyana cewa Shittu na daya daga cikin ministocin da aka gargadi shugaba Buhari kada ya sake nadawa saboda matsalolin da ke fuskanta na tsangwama da zarge-zargen badakala.

Majiyar ta kara da cewa Shittu ka iya zama matsala ga APC a jihar Oyo idan Buhari ya nadasa.

Ta fara bayyana: Sunan daya daga cikin ministocin da ba zasu dawo ab ya bayyana

Ta fara bayyana: Sunan daya daga cikin ministocin da ba zasu dawo ab ya bayyana
Source: Depositphotos

Daga cikin matsalolin da Shittu ke fuskanta shine zargin cewa bai yi bautar kasa ba, sannan kuma kararsa da wasu tsaffin hadimansa suka kai kotu kan rashin biyansu albashinsu.

A ranar Talar, an kai karan Shittu kotun ma'aikata kan kudi milyan ashirin da daya da dari biyar (N21,500,000.00) na albashi da alawus.

Wadanda suka shigar da shi kara sune tsohon hadiminsa, Razaq Olubodun da tsohon mai magana da yawunsa, Victor Oluwadamilare.

KU KARANTA: EFCC ta maka wani dan kasuwa kotu akan badakkalar N115m

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel