Buhari ya sha ruwa da masu bukata ta musamman, ya zuba musu abinci da hannun sa

Buhari ya sha ruwa da masu bukata ta musamman, ya zuba musu abinci da hannun sa

A ranar Alhamis, 23 ga watan Mayu ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha ruwa tare da wasu 'yan Najeriya masu bukata ta musamman a fadar gwamnatin tarayya dake Abuja.

Yayin shan ruwan, an ga shugaba Buhari da kan sa yana zuba abinci tar da mika wa ga masu bukata ta musamman kasancewar wasu daga cikin su nada nakasar kafafu (guragu) da ta saka ba zasu iya mike wa tsaye ba.

Bisa ga al'ada, shugaba Buhari kan sha ruwa tare da kungiyoyi daban-daban a kowacce rana a cikin watan Ramadana.

Hatta lokacin da ya yi tafiya zuwa kasar Saudiyya, shugaba Buhari ya karbi bakuncin wasu 'yan Najeriya tare da shan ruwa tare da su.

Buhari ya sha ruwa da masu bukata ta musamman, ya zuba musu abinci da hannun sa

Buhari ya sha ruwa da masu bukata ta musamman, ya zuba musu abinci da hannun sa
Source: Twitter

Sanannu daga cikin irin mutanen da shugaba Buhari ya sha ruwa tare da su a kasar Saudiyya sun hada da gwamnan jihar Zamfa, Abdulaziz Yari, wanda ya ziyarci shugaba Buhari tare da sarkin Maradun.

DUBA WANNAN: Kwangen haraji: Jerin bankuna 16 da majalisa tayi umarnin a hukunta

Bola Tinubu, jagoran jam'iyyar APC na kasa, mai alfarma sarkin Musulmi, Sa'ad Abubakar III, sarkin Kazaure, Najib Hussaini Adamu, na daga cikin mutanen da suka sha ruwa tare da shugaba Buhari a kasar Saudiyya.

Bayan dawowar sa gida Najeriya, shugaba Buhari ya cigaba da karbar bakuncin kungiyoyi domin shan ruwa tare da su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel