Jihohi 14 sun ki amincewa da shirin kula da lafiyar al'ummar su

Jihohi 14 sun ki amincewa da shirin kula da lafiyar al'ummar su

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi zargin cewa, akwai wasu jihohi 14 a kasar nan da suka kauracewa shiga shirin kula da lafiya zai ba su damar amfana da makudan dukiyar kasa da aka ware da manufa ta kula da lafiyar al'ummomin su.

Ministan Lafiya Isaac Adewole

Ministan Lafiya Isaac Adewole
Source: Facebook

Ministan lafiya na kasa Isaac Adewole, shi ne ya bayar da shaidar hakan a zauren majalisar dattawa da cewar a halin yanzu akwai jihohi 22 da suka yi rajistar cin moriyar shirin kuma tuni gwamnati ta antaya masu kudaden kai tsaye zuwa cibiyoyin kula da lafiyar su a matakai daban daban.

Kamar yadda Ministan Lafiya na Najeriya ya bayyana, jihohin da suka kauracewa shiga domin cin moriyar shirin kula da lafiyar al'ummomin su sun hadar da; Sakkwato, Jigawa, Benuwai, Taraba, Nasarawa, Zamfara, Kebbi, Ondo, Cross River, Ogun, Akwa Ibom da kuma Borno.

KARANTA KUMA: Buhari ya karbi sabbin jakadu daga kasar Isra'ila da Sierra Leone a fadar Villa

Jaridar RFI Hausa ta ruwaito cewa, sharuddan cin gajiyar shirin da gwamnatin tarayya tayi tanadi sun hadar da kafa hukomomin kula da lafiya a mataki na farko da kuma assassa shirin inshorar lafiya ta jiha gami zuba wasu kudade a asusun kula da lafiya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel