Shugabancin majalisa: Tinubu da Goje sun gana a kasar Saudiyya

Shugabancin majalisa: Tinubu da Goje sun gana a kasar Saudiyya

- Babban jigon jam’iyyar APC na kasa, Asiwaju Bola Tinubu da Sanata Danjuma Goje sun gana a kasar Saudiyya

- An tattaro cewa ganawar baya rasa nasaba da takarar shugabancin majalisar dattawa

- Shugabancin jam’iyyar ta zabi Sanata Ahmed Lawan a matsayin dan takarar da ta fi so ya haye matsayin

Rahotanni da ke zuwa mana daga jaridar Independent ya nuna cewa Sanata Danjuma Goje da babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, sun yi ganawar sirri a kasar Saudiyya kan shugabancin majalisar dattawa.

Legit.ng ta tattaro cewa daga Tinubu har Goje suna kasar Saudiyya a yanzu haka inda suke aikin Umurah.

Goje ya kasance babban abokin adawar Ahmed Lawan wajen neman shugabancin majalisar dattawan.

Shugabancin majalisa: Tinubu da Goje sun gana a kasar Saudiyya

Shugabancin majalisa: Tinubu da Goje sun gana a kasar Saudiyya
Source: UGC

Daga Tinubu har APC sun riga da sun nuna goyon bayansu ga Lawan tun farko.

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa, akwai alamu dake nuna cewa jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zata tsayar da dan takara a shugabancin majalisar dattawa, idan har sanata Danjuma Goje (APC Gombe ta tsakiya) ya janye daga yin takara.

KU KARANTA KUMA: Aisha Buhari za ta gana da mata da yara gabanin rantsar da shugaban kasa

Majiyoyi na kusa da majalisar dattawa sun bayyana ma New Telegraph a karshen makon da ya gabata cewa jam’iyyar PDP na sanya ido akan yanayin al’amura, don ganin abunda zai faru a jam’iyyar APC, dangane da wadanda zasu tsaya takara a jam’iyya mai ci kafin ta yanke shawara akan ko ta tsaya takara.

A cewar daya daga cikin majiyan, tunda Goje ya ki bayyana ra’ayin shi na neman shugabancin majalisar dattawa ga al’umma, jam’iyyar adawa na jiran lokaci mafi dacewa don yanke shawara akan lamarin.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel