Shugabanin Neja-Delta sun mika wata babban bukatarsa ga Buhari

Shugabanin Neja-Delta sun mika wata babban bukatarsa ga Buhari

Manyan shugabanin yankin Neja Delta sun bukaci Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada dan jihar Delta a matsayin shugaban Hukumar Cigaban Yankin Neja-Delta (NDDC).

Sun ce hakan zai taimaka wurin tabbatar da hadin kai da zaman lafiya a yankin.

A cikin wasikar da suka aike wa shugaban kasar, shugabanin Neja-Deltan sun ce sun cimma matsaya kan wanda suke son a nada ya jagoranci hukumar saboda kaucewa rikici bayan nadin shugaban na NDDC.

Shugabanin Neja Delta sun nemi wata babban alfarma a hannun Buhari

Shugabanin Neja Delta sun nemi wata babban alfarma a hannun Buhari
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Gwamna Yari ya yi watsi da jama'arsa ya tare a Abuja - Wani sanata ya yi korafi

Cikin wasikar mai dauke da sa hannun shugaban kungiyar, Bestman Odibo da Sakataren yada labaran kungiyar, Christopher Orushani, shugabanin sun roki Buhari ya yi adalci wurin nadin 'yan kwamitin hukumar ta NDDC.

Kungiyar ta ce jihohin Bayelsa, Rivers da Akwa Ibom duk sunyi shugabancin hukumar saboda haka yanzu lokaci ne na jihar Delta.

Sun jadada cewa za a cigaba da karba-karba ne tsakanin jihohin amma dai a yanzu jihar Delta ce ya dace ta fitar da shugaban hukumar.

Wani sashi na wasikar ya ce, "Kamar yadda ya ke cikin dokar da ta kafa NDDC, ana nadin shugaban hukumar na tsakanin jihohin da ke samar da man fetur inda aka fara da jihar da ta fi sauran samar da man fetur. Idan za ayi la'akari da dokar Jihar Delta ce za ta fitar da shugaban bayan Akwa-Ibom."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel