Aisha Buhari za ta gana da mata da yara gabanin rantsar da shugaban kasa

Aisha Buhari za ta gana da mata da yara gabanin rantsar da shugaban kasa

Uwargidan shugaban kasa, Hajiya Aisha Buhari za ta gana da matan Najeriya da kananan yara a ranar Asabar 25 ga watan Mayu domin tattaunawa kan sabbin hanyoyin inganta rayuwarsu.

Taron zai mayar da hankali ne a kan inganta shigar mata cikin siyasa da kuma hanyoyin inganta lafiya da motsa jiki na mata da yaran.

Hajiya Mariya Rufai, sakatariyar karamin kwamitin uwargidan shugaban kasa na shirye-shiryen bikin kaddamar da shugaban kasa na shekarar 2019 ne ta bayar da wannan sanarwar a ranar Alhamis a Abuja.

Aisha Buhari za ta gana da mata da yara gabanin rantsar da shugaban kasa

Aisha Buhari za ta gana da mata da yara gabanin rantsar da shugaban kasa
Source: Depositphotos

DUBA WANNAN: Gwamna Yari ya yi watsi da jama'arsa ya tare a Abuja - Wani sanata ya yi korafi

Ta kuma sanar da cewa uwargidan shugaban kasar za ta shirya liyafa domin yara a dakin taro na gidan gwamnati da ke Abuja.

Uwargidan shugaban kasar tana daya daga cikin wadanda suka dade suna fafutikan neman inganta lafiyar mata masu juna biyu da kananan yara a Najeriya.

Sauran ayyukan da Aisha ta ke yi sun hada da inganta ilimin yara mata, tallafawa matasa samun ingantaccen ilimi da kuma wayar da kan matasa da mata kan illar muggan kwayoyi kamar yadda NAN ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel