EFCC da INTERPOL na daf da kama Abdulrashid Maina a maboyar sa a kasar waje

EFCC da INTERPOL na daf da kama Abdulrashid Maina a maboyar sa a kasar waje

- Rahotanni sun bayyana cewar hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki na daf da kama tsohon shugaban hukumar fansho ta kasa, Abdulrashid Maina

- Wata majiya a EFCC da ta nemi a boye sunanta ta ce wasu kwararrun ma'aikatan hukumar na bibiyar al'amuran Maina

- Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da tsohon mataimakin sakataren yada labaran jam'iyyar APC, Timi Frank, ya bukaci majalisar dattijai ta bayya rahoton sakamakon binciken Maina

Rahotanni sun bayyana cewar hukumar yaki da cin hanci da karya tattalin arziki (EFCC) ta hada kai da jami'an 'yan sandan Najeriya dake aiki a kasashen ketare domin kama tsohon shugaban kwamitin bawa shugaban kasa a kan gyaran harkar fansho a kasa, AbdulRasheed Maina.

Wata majiya a EFCC ta sanar da wakilin Legit.ng a jihar Kaduna, Nasir Dambatta, cewar Maina na da tuhumar da ya kamata a gaban kotu kuma tun bayan guduwar sa jami'an hukumar na musamman da lauyoyinta ke bibiyar shari'ar a gaban kotu.

Rahotannin sakamakon bincike da dama sun bukaci a binciki Maina a kan badakalar biliyoyin kudin 'yan fansho.

EFCC da INTERPOL na daf da kama Abdulrashid Maina a maboyar sa a kasar waje

AbdulRashid Maina
Source: UGC

Ko a cikin satin da ya gabata sai da tsohon mataimakin sakataren yada labaran jam'iyyar APC, Timi Frank, ya bukaci majalisar dattijai ta bayya rahoton sakamakon binciken da ta gudanar a kan zargin da ake yiwa Maina a kan batar da biliyoyin kudin 'yan fansho.

A cikin shekarar da ta gabata ne aka samu barkewar cece-kuce bayan wasu rahotanni sun yi ikirarin cewar an mayar da Maina bakin aiki har ma an yi masa karin girma.

DUBA WANNAN: Kwangen haraji: Jerin bankuna 16 da majalisa tayi umarnin a hukunta

A cikin wasu watanni da suka wuce ne kafafen yada labarai suka wallafa wani rahoto dake cewa EFCC ta gano wani asusun 'yan fanshon Najeriya a kasar Ingila, kuma ta fara bincike domin gano yadda kudin 'yan fansho a Najeriya ya zurare zuwa kasar.

A 'yan kwanakin baya bayannan ne aka rawaito cewar Maina ya nuna sha'awar sa ta dawowa Najeriya domin tona asirin makudan biliyoyin kudin fansho da aka sace matukar shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bashi tabbacin tsaron lafiyar sa, bukatar da aka ce shugaba Buhari ya yiwa kunnen uwar shegu.

Duk da babu wani sahihin labari dangane da kasar da Maina yake a boye, kokarin majiyar mu na tuntubar sa a kan wannan batu, ta hanyar kiran lambar sa ta waya, bai samu ba har zuwa lokacin da aka wallafa wannan rahoto.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel