Badakalar kudi: Kotun tarayya ta bayar da umarnin kama tsohon Gwamna Aliyu

Badakalar kudi: Kotun tarayya ta bayar da umarnin kama tsohon Gwamna Aliyu

- Kotu ta janye belin da aka bawa tsohon gwamnan jihar Neja, Babangida Aliyu da Umar Nasko

- An janye belin ne sakamakon rashin gurfana a gaban kotu da ba suyi ba domin cigaba da saurarn shari'ar da ake musu na zambar Naira biliyan 1.9

- Kotun ta kuma bayar da umurnin a kamo Babangida Aliyu da Umar Nasko ba tare da bata lokaci ba

PDP: Kotun tarayya ta bayar da umarnin kama tsohon gwamna Aliyu

PDP: Kotun tarayya ta bayar da umarnin kama tsohon gwamna Aliyu
Source: Depositphotos

Alkalin kotun tarayya da ke Minna, Jastis Aminu Aliyu, a ranar Alhamis 23 ga watan Mayu, ya bayar da umurnin kamo tsohon gwamnan Jihar Niger, Babangida Aliyu da Umar Nasko.

Jastis Aliyu ya kume janye belin da Jastis Yellim Bogoro ya bawa Aliyu da Nasko saboda rashin bayyana a kotu domin cigaba da sauraron shari'ar da ake musu.

DUBA WANNAN: An roki Buhari ya ajiye Lai Mohammed a karo na biyu

Kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN), ta ruwaito cewa kotu ta bukaci Aliyu da Nasko su gurfana a gabanta a ranar Alhamis ne domin sake fara sauraron shari'ar tuhumar da ake musu na damfarar Naira Biliyan 1.9 da aka mayar zuwa kotun Jastis Aliyu.

Lauyansu shima bai bayyana a gaban kotu ba.

Olajide Ayodele, lauyan Gwama Aliyu, ya aike wa kotu da wasika inda ya roki a dage cigaba da sauraron karar.

Daga karshe an dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 27 ga watan Mayun 2019 kamar yadda NAN ta ruwaito.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku Latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel