Kwangen haraji: Jerin bankuna 16 da majalisa tayi umarnin a hukunta

Kwangen haraji: Jerin bankuna 16 da majalisa tayi umarnin a hukunta

Majalisar wakilai ta bukaci a hukunta wasu bankunan Najeriya 16 saboda kin saka zunzurutun kudin harajin kan sarki (stamp) da yawan su ya kai biliyan N1.6 a asusun gwamnatin kasa.

Majalisar ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis bayan sauraron rahoton kwamitin binciken tiriliyoyin kudin harajin amfani da kan sarki da ma'aikatu da cibiyoyin harkokin kudi suka ki biyan gwamnatin tarayya.

Mamba a majalisar, Abubakar Ahmad (dan jam'iyyar APC daga jihar Adamawa), ne ya gabatar da rahoton kwamitin a zauren majalisar yayin zaman ta na ranar Alhamis a Abuja.

Majalisar ta kafa kwamitin na wucin gadi ne domin zakulo cibiyoyi, masana'antu da kamfanonin harkokin kudi dake yiwa gwamnatin tarayya kwange wajen biyan kudin harajin amfani da kan sarki.

Kwangen haraji: Jerin bankuna 16 da majalisa tayi umarnin a hukunta

Majalisar wakilai
Source: Twitter

Rahoton kwamitin ya bukaci a hukunta bankunan tare da tilasta su biyan adadin kudin da gwamnati ke bin su na tsawon lokacin da basu biya harajin ba.

Ga jerin bankunan majalisar ke son a hukunta da kuma adadin kudin haraji da gwamnati ke bin su – "Guarantee Trust Bank (GTB) N198,326,300, Standard Chartered Bank, N3,658,193, Citi Bank N1,860,850 da Standard IBTC N231,094,565.

DUBA WANNAN: Abinda yasa muke samun nasara a yaki da 'yan bindiga a Sokoto - Kwamandan sojoji

"Ragowar su ne; Zenith Bank N265,635,650, Providus Bank N646,650, Fidelity Bank N32,888,400, Keystone Bank N24,471,050 and UBA N81,087,149.

"ECO Bank N78,527,004, Diamond Bank (wanda ya koma Access Bank) N545,873,950, Unity Bank N40,099,100 and Jaiz Bank N2,436,150.

Sai Access Bank N66,092,350, Skye Bank N11,057,700 da Polaris Bank N2,907,550,” kamar yadda ake a cikin rahoton.

Kazalika, rahoton kwamitin ya yaba wa bakunan First Bank Plc, First City Monument Bank (FCMB), Wema Bank da Suntrus Bank bisa kokarin biyan haraji a kan lokaci.

Majalisar ta bayyana cewar za ta turo rahoton wurin shugaban kasa domin zartar da hukuncin da ta bukaci a yiwa bankunan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel