Buhari ya gana da gwamnoni 36 na Najeriya a fadar Villa

Buhari ya gana da gwamnoni 36 na Najeriya a fadar Villa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis, 23 ga watan Mayun 2019, ya yi ganawar sirrance tare da gwamnoni talatin da shida na Najeriya cikin fadar sa ta Villa dake babban birnin kasar nan na tarayya.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa, ganawar da shugaban kasaBuhari ya jagoranta cikin babban dakin taro na Council Chambers dake fadar Villa ta gudana ne domin tabbatar da nadin sabon sufeto janar na 'yan sanda, Muhammad Adamu.

Buhari ya gana da gwamnoni 36 na Najeriya a fadar Villa

Buhari ya gana da gwamnoni 36 na Najeriya a fadar Villa
Source: Twitter

Ko shakka babu kafofin watsa labarai da dama sun ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari yayin ganawa a zaman na majalisar hukumar 'yan sanda da ta hadar da dukkanin gwamnonin kasar nan da kuma sauran masu ruwa da tsaki, ta tabbatar da nadin mukamakin sufeto janar na 'yan sanda.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya jagoranci zaman majalisar tattalin arziki na bankwana tare da gwamnoni talatin da shida a babban dakin taro na fadar shugaban kasa.

KARANTA KUMA: Dalilin da ya sa na maka Sufeton 'Yan sanda a kotu - Adeleke

Kazalika a ranar Larabar da ta gabata ne shugaban kasa Buhari ya jagoranci zaman majalisar zantarwa na bankwana tare da dukkanin 'Ministocin sa inda ya ba su umurnin sauka daga kujerun su a ranar jajibirin rantsar da shi kan gadon mulki a wa'adin gwamnatin sa na biyu.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel