Firai Ministan Birtaniya, Theresa May, za ta yi murabus a ranar Juma'a

Firai Ministan Birtaniya, Theresa May, za ta yi murabus a ranar Juma'a

Rahotanni da ke zuwa mana a yanzu daga kafofi daban daban na jaridun kasar Birtaniya, sun tabbatar da cewa, akwai yiwuwar Firai Ministan kasar, Theresa May, za ta yi murabus daga kujerar mulki a ranar Juma'a.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, sauka daga gadon mulki na Firai minista Theresa zai janyo wawaso da kururuwa ta hankoron maye gurbin ta a tsakankanin manyan ministoci na jam'iyya mai ci ta kasar, Conservative.

Firai Ministan Birtaniya, Theresa May

Firai Ministan Birtaniya, Theresa May
Source: Twitter

Kafofin watsa labarai na kasar sun bayyana cewa, murabus din Firai minista Theresa zai bude sabon shafi na ci gaba da tattaunawa kan maslahar majalisar Birtaniya kan yadda kasar za ta fice daga kungiyar Tarayyar Turai, EU.

Wani sabon tasgaro da zai tunzura Firai Minista Theresa sauka daga kujerar mulki ya auku a daren Laraba yayin da daya daga cikin manyan magoyan bayan ta kan akidar ficewa da kungiyar Tarayyar Turai, Andrea Leadsome, tayi murabus.

KARANTA KUMA: Buhari ya gana da gwamnoni 36 na Najeriya a fadar Villa

Bayan kasa samun nasarar a karo uku daban daban kan yarjejeniyar da Firai Minista Theresa May ta amince tsakaninta da Tarayyar Turai, da yawa daga cikin 'yan majalisar ta na jam'iyyar Conservative sun juya mata baya.

Da yawa daga cikin 'yan majalisar Birtaniya na jam'iyyar DUP da Firai Minista Theresa ta dogara kan samun goyon bayan su sun ki sauya matsayar su ta rashin goyon bayan ficewar kasar Birtaniya daga Tarayyar Turai.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel