Boko Haram: Malamai 2,295 sun hallaka, 19,000 sun rasa muhallinsu a Borno, Yobe da Adamawa, da sauran jihohi - Ministan Ilimi

Boko Haram: Malamai 2,295 sun hallaka, 19,000 sun rasa muhallinsu a Borno, Yobe da Adamawa, da sauran jihohi - Ministan Ilimi

- Malam Adamu Adamu ya bayyana abinda ya kara yawan yara marasa zuwa makaranta

- Ya nemi afuwa bisa ga gazawarsa wajen cika alkawarin da ya yiwa yan Najeriya yayinda wa'adinsa ya kare

Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, ya bayyana cewa cikin shekaru tara akalla malaman makaranta 2,295 suka rasa rayukansu yayinda 19,000 suka rasa muhallansu sakamakon rikicin Boko Haram a jihohin Borno, Yobe da Adamawa.

Kana a cewarsa, akalla makarantu 1500 Boko Haram ta lalata daga shekarar 2014 zuwa yanzu. Ya ce wannan ya taimaka wajen yawan yara maras zuwa makaranta a fadin tarayya.

KU KARANTA: Yanzu-Yanzu: An tabbatar da mukaddashin IG Adamu a matsayin Sifeto Janar na yan sanda

A jawabinsa yace: "Babban kalubalen rashin karatun yara a shekarun kusa-kusan nan, matsalar rashin tsaro. Tun lokacin da matsalar tsaro ya fara a yankin Arewa maso gabas, bangaren ilimi ya fara fuskantar kalubale na kisan dalibai da malamai, da kuma lalata makarantu."

"Akalla iyaye 2,295 aka kashe, 19,000 sun rasa muhallansu a jihohin Borno, Yobe, da Adamawa cikin shekaru tara da suka gabata. kimanin makarantu 1,500 aka lalata tun shekarar 2014."

"Wannan rikici ya kara lalata harkar ilimi yayinda yara dalibai, malamai da makarantu babban abin hari."

Domin magance haka, ministan ya ce ma'aikatar ilimi tare da hannin kan kungiyoyin UNESCO, UNICEF, diraktocin cibiyoyin bincike da lissafi na yankunan Najeriya shida sun kirkiro wani kudiri na kare yara dalibai da rikice-rikicen rashin tsaro.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Nigeria

Tags:
Mailfire view pixel