EFCC ta maka wani dan kasuwa kotu akan badakkalar N115m

EFCC ta maka wani dan kasuwa kotu akan badakkalar N115m

-EFCC ta shiga kotu da wani hamshakin dan kasuwar man fetur bisa zarginsa da almundahanar N115m.

-Alkalin babbar kotun kasa dake Abuja ya dage sauraron karar har zuwa watan Yuli domin bangaren wadanda ake tuhuma su yi shirin kare kansu daga zargi.

Babbar kotun kasa dake birnin Abuja ta aikawa da wani hamshakin dan kasuwar man fetur Emmanuel Owoicho da sammaci tare da wasu mutum uku akan tuhumarsu da ake da almundahanar N115m.

Hukumar yaki da cin hanci da kuma yiwa tattalin arziki zagon kasa ta EFCC it ace ta shigar da wannan kara inda take tuhumar Owoicho, Taiye da kuma Michael Oghenemi da laifuka 12 ciki hadda mallakar takardun bogi.

EFCC ta kai wani hamshakin mai kasuwancin man fetur kotu akan tuhumarsa da almundahanar N115m

EFCC ta kai wani hamshakin mai kasuwancin man fetur kotu akan tuhumarsa da almundahanar N115m
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Madalla: An kama ‘yan baranda 20 a jihar Sokoto

Jastis Peter Affen wanda shi ne alkalin kotun yace sam babu wata maganar watsi da kara kamar yadda lauyoyin dake kare wadanda ake kara suka nema.

“ Babu dalilin da zai sa mu yi watsi da kara. Adon haka kuma dake kariyar wanda ake tuhuma sai dai ku bude naku daftarin domin shigar da jawabanku ga kotu.” Inji alkalin kotun.

Hukumar EFCC tana tuhumar Owoicho ne tare da abokansa akan cinikin sayar da Bonny Light crude oil inda suka ce mallakar kamfanin tatar mai na kasa ne wato NNPC zuwa ga Bascom Energy Limited akan kudi N115m.

Bugu da kari, akwai wasu laifuka da dama da hukumar ke tuhumar wadannan mutane akai ciki akwai na karbar kudade lokuta da dama kan cewa zasu kawo man fetur amma kuma basu kawo ma wanda ya basu kudin komi.

Alkalin kotun ya dage sauraron karar har zuwa 3 ga watan Yuli domin wadanda ke kariyar wanda ake tuhuma su shirya kalubalantar kararsu da aka shigar.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel