Yanzu-Yanzu: An tabbatar da mukaddashin IG Adamu a matsayin Sifeto Janar na yan sanda

Yanzu-Yanzu: An tabbatar da mukaddashin IG Adamu a matsayin Sifeto Janar na yan sanda

An tabbatar da mukaddashin Sifeto Janar na hukumar yan sandan Najeriya, Muhammad Adamu, a matsayin sifeto janar na din-din-din a ranar Alhamis, 22 ga wtaan Mayu, 2019 a fadar shugaban kasa dake birnin tarayya Abuja.

An tabbatar da IGP Adamu ne a wani taro na musamman da shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta da kansa.

Shugaban ma'aikatan hukumar yan sanda, Musuliu Smith, da gwamnonin Najeriya 36 ne suka halarci wannan muhimmin taro.

IGP Adamu ya dau ragamar mulkin hukumar yan sandan ne a 15 ga watan Junairu, 2019 daga hannun magabacinsa, Ibrahim Idris.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel