Kashe kashen Binuwe: BMO surutu kawai ta iya, inji Dakta Wayas

Kashe kashen Binuwe: BMO surutu kawai ta iya, inji Dakta Wayas

-Wani lakcara daga jami'ar Najeriya dake Nsukka ya caccaki BMO akan kashe-kashen dake addabar jihar Binuwe.

-Dakta David Wayas yace, kungiyar bata iya komi ba ila surutu maras amfani.

Wani lakcara dake bangaren nazarin ilimin harsuna na jami’ar Najeriya dake Nsukka, Dakta David Wayas yayi kaca-kaca da kungiyar Buhari dake kula da shafukan sadarwa wato Buhari Media Organization (BMO), a turance akan tashin hanakalin dake addabar jihar Binuwe.

Wayas yace a maimakon wannan kungiyar ta maida hankalinta wurin ba shugaba Buhari shawarwari akan jagorancin wannan kasa, sai bata yi hakan ba inda ta tsaya yin abinda ba shikenan ba domin ta samu karbuwa wurin jama’a.

Kashe kashen Binuwe: BMO surutu kawai ta iya, inji Dakta Wayas

Kashe kashen Binuwe: BMO surutu kawai ta iya, inji Dakta Wayas
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Boko Haram ta kai harin da yayi sanadiyar rai guda da kuma batar mutum 6 a sansanin soji dake Gubio

Daktan wanda ya zanta da ‘yan jarida daga ofishinsa a ranar Laraba yace, kuskure ne babba ga wannan kungiya da ta jingina wannan kashe-kashe zuwa ga gwamnan jihar Binuwe Samuel Ortom.

“ Ba komi bane wannan face hada rigima da kuma tayar da zaune tsaye a tsakanin mazauna jihar Binuwe. Abinda ya faru daban, abinda suke fadi wa mutane kuma daban.” Inji David.

Har ila yau Daktan yayi karin haske kan cewa, gwamna Ortom yayi nasarar lashe zabe ne a karo na biyu saboda nuna damuwa da yake yi a cikin al’amuran jama’ar jiharsa. Dalilin hakan ne ma yasa ya kaddamar da sabuwar dokar hana kiwon dabbobi sakaka saboda samun maslahar rikicin Fulani da manoma a Binuwe.

“ A lokacin da gwamnatin jihar Binuwe ta kaddamar da wannan doka ta hana yin kiwo, yan kungiyar Miyetti Allah sun yi bore daga bisani suka bi mutanenmu suka karkashe.”

“ BMO kawai wata kungiyace wacce bata da aiki sai shaci fadi da yada labarin abinda bai faru ba. Ya zama dole in yabawa shugaba Buhari saboda bai sanya bakinsa cikin zaben jihar Binuwe ba a zaben da ya gabata na 2019.” A fadar David.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel