Yan gudun hijira na cikin tashin hankali saboda yunwa, 8 sun mutu

Yan gudun hijira na cikin tashin hankali saboda yunwa, 8 sun mutu

Mutane 8 ne suka ragimu gidan gaskiya a sansanin yan gudun hijira dake Mbawa na jahar Benuwe daga watan Janairu zuwa watan da muke ciki, kamar yadda kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito cewa shugaban sansanin, Geoffrey Torgenga ne ya bayyana haka a ranar Laraba, 22 ga watan Mayu a garin Makurdi yayin da yake ganawa da manema labaru, inda ya danganta mutuwar yan gudun hijiran ga matsanancin yunwa.

KU KARANTA: Kashe kashe: Akalla Sakkwatawa da Zamfarawa 20,000 sun yi gudun hijira zuwa Nijar

Torgenga ya kara da cewa baya ga yunwa, yan gudun hijira sun fama da yaduwar wasu cututtuka a sansaninsu dake kauyen Daudu, cikin karamar hukumar Guma, yace mutuwar da suka samu ta kwana kwanan nan itace wanda aka yi a karshen makon data gabata.

Rahotanni sun bayyana lokacin karshe da gwamnati ta aika da kayan abinci zuwa sansanin shine a watan Feburairu, lokacin da zabukan shugaban kasa, gwamnoni dana yan majalisu ke karatowa kenan.

Don haka shugaban sansanin yace a yanzu haka yan gudun hijira da suka kai 3,515 sun dangana ne kawai ga taimakon da kungiyoyin sa kai, kungiyoyin addinai, da kuma jama’an gari suke kai musu a duk lokacin da suka samu dama.

Torgenga ya bada misalin wani karamin yaro dan shekara 3, Nani Iyorkaa wanda yake zuwa daji don roro itatuwan da yake sayarwa yana samun na abinci, inda yace a yanzu haka yaron ya bace tun wata fita da yayi nemo itace, dama sana’ar da wasunsu suke yi kenan don ciyar da kansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel