Yan sandan Jigawa sun kama yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran laifuffuka su 27

Yan sandan Jigawa sun kama yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran laifuffuka su 27

Rundunar yan sandan Jigawa sun kama masu laifi 27 kan zargin aikata laifuffuka daban-daban. Abdu Jinjiri, kakakin yan sandan jihar, ya bayyana hakan a wani jawabi da ya saki a garin Dutse a ranar Alhamis, 23 ga watan Mayu.

Mista Jinjiri yace anyi kamun ne bayan mukaddashin sufeto janar na yan sanda, Mohammed Abubakar, ya kaddamar da atisayen `Operation Puff Adder’ a jihar tare da kudirin yakar manyan laifuka a yankin.

Yayi bayanin cewa Mista Adamu ya umurci kwamishinonin yan sanda da su kaddamar da makamancin haka a jihohinsu.

Kakakin yan sandan ya kara da cewa hukumar ta dauki wasu matakan tsaro kamar sanya ido, kai mamaya wuraren ta’addanci, da uma sintiri sosai, sannan ta hada kai da sauran hukumomin doka da jama’a, sakamakon haka ne rundunar ta cimma wadannan nasarori.

Yan sandan Jigawa sun kama yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran laifuffuka su 27

Yan sandan Jigawa sun kama yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran laifuffuka su 27
Source: Depositphotos

Mista Jinjiri yace biyu daga cikin mutanen da aka kama ana zarginsu da hada kai wajen garkuwa da mutane.

Ya kara da cewa an kama masu garkuwa da mutanen ne bayan wasu yan fashi sun sace wani one Adre Palsin, dan kasar Indiya mai aiki da kamfanin gine-gine na Alren a ranar 18 ga watan Maris, a karamar hukumar Jahun da ke jihar.

KU KARANTA KUMA: Ayyukan yan bindiga: Daraktan Kannywood, Falalu Dorayi yayi kira ga yan arewa da su kare kansu

Ya kuma bayyana cewa 21 daga cikin masu laifin an kama su ne kan zargin aikata ayyukan laifi da kuma fashi a karamar hukumar Dutse.

A cewarsa, hudu daga cikinsu an kama su ne a karamar hukumar Dutse kan zargin karban kayayyakin sata da kuma ajiye kayan sata.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Online view pixel