Kuma dai, ‘yan Najeriya 195 sun dawo gida daga Libya bayan sun galabaita

Kuma dai, ‘yan Najeriya 195 sun dawo gida daga Libya bayan sun galabaita

-An sake dawo da wani ayarin yan Najeriya mai kunshe da mutane 195 gida daga kasar Libya bayan da suka galabaita.

Wata tawagar yan Najeriya mai kunshe da mutum 195 ta dawo gida daga Libya bayan da suka riga suka galabaita.

Yawan wadannan mutanen ya zarce dukkanin ayarin masu dawo Najeriya daga Libya tun shekarar 2017 da aka soma dawo da su.

Kuma dai, ‘yan Najeriya 195 sun dawo gida daga Libya bayan sun galabaita

Kuma dai, ‘yan Najeriya 195 sun dawo gida daga Libya bayan sun galabaita
Source: Depositphotos

KU KARANTA:Boko Haram ta kai harin da yayi sanadiyar rai guda da kuma batar mutum 6 a sansanin soji dake Gubio

Hukumar kula da bayar da taimakon gaggawa ta NEMA ce ta karbi mutanen tare da jam’in gwamnatin Najeriya a filin sauka da tashin jiragen sama na Murtala Muhammad dake Legas.

Daga cikin hukumomin da suka taho da wannan tawagar akwai hukumar kula da shige da fice ta Immigration, hukumar kula da yan gudun hijira ta kasa da sauran hukumomin da al’amarin ya shafa.

Shugaban hukumar NEMA reshen jihar Legas ya shaida wa manema labarai cewa wannan tawagar da ta dawo it ace ta 69 da aka kawo Najeriya karkashin kulawar International Organization for Migration (IOM) wato kungiyar dake kula da hijira ta duniya.

Jirgin Alburak shine ya dauka wadannan mutane daga garin Sabha yayin da irgin mai dauke da lamba kamar haka UZ 389/22 ya dira filin jirgin Ikeja da misalign karfe 8:20 na marecen Laraba.

Daga cikin mutanen da aka dawo da su gida, 71 mata ne manya, 25 kuma yan mata ne sai kuma 17 kananan yara mata.

Bugu da kari, 60 maza ne baligai, 12 kuma matasa maza sai kananan yara maza guda 10. A jimilla mata sun kama 113 yayinda maza suka kama 82. 131 ne baligai a ciki, 37 matsa ne sai kuma 27 yara kananan akwai mutum 3 masu rashin lafiya sai kuma mata 7 masu dauke da juna biyu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel