Tsohon ministan ayyuka ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

Tsohon ministan ayyuka ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

Wani tsohon ministan ayyuka, Sanata Adeseye Ogunlewe, a jiya Laraba, 22 ga watan Mayu, ya sauya sheka daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Legas.

Ya bayyana sauya shekar tasa ne a taron jiga-jigan APC, maai taken The Mandate Movement (TMM).

Ya bi dansa, Moyosore wajen barin jam’iyyar PDP zuwa APC.

Yayin da yake magana a taron, Ogunlewe yace: “kada kowa yayi tsammanin dan siyasa kamar ni ya tsaya a gidan da wassu masu jagora ke damuwa da kansu.”

Tsohon ministan ayyuka ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

Tsohon ministan ayyuka ya sauya sheka daga PDP zuwa APC
Source: UGC

Ogunlewe har ila yau yace shima zai shiga APC ne saboda ya gamsu cewa Jam’iyyan zata raba shugabancin kasa zuwa ga yankin Kudu maso Yamma a 2023, bayan kasancewarta jam’iyya mafi nagarta.

Ogunlewe yace ba zai so a bar shi ba a baya wajen gudanar da shirin baiwa yankin shugabancin kasa a 2023.

KU KARANTA KUMA: Ayyukan yan bindiga: Daraktan Kannywood, Falalu Dorayi yayi kira ga yan arewa da su kare kansu

Shuwagabannin TMM wadanda suka tarbe shi sun hada da mataimakin shugaban jam’iyyan APC, yankin mazabar gabashin Legas a majalisan dattawa, Asioa Kaoli Olusanya, babban jigon APC, Cif Adenrele Olowu, mamba a majalisan dokokin kasa kuma tsohon kwamishinan yawon bude ido, fasaha da al’adu, Adebimpe Akinsola, jigon APC, Alhaji S. Musa, shuwagabannin kungiyar APC, da sauran shuwagabannin TMM.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel