AAC ta kafa kwamitin binciken Sowore kan wasu makudan kudade

AAC ta kafa kwamitin binciken Sowore kan wasu makudan kudade

-Shugaban jam'iyar AAC na kasa zai fuskanci bincike akan zarginsa da almundahanar wasu kudi.

-Majalisar zartarwar jam'iyar AAC ta baiwa kwamitin bincike mako guda domin ya kawo mata rahoto akan wannan lamarin.

Majalisar masu zartarwa na jam’iyar African Action Alliance (AAC) ta kafa wani kwamiti domin ya binciki Omoyele Sowore kan zargin da ake yi masa na karbar $1m a lokacin zaben gwamnan jihar Ribas.

AAC ta kafa kwamitin binciken Sowore kan wasu makudan kudade

AAC ta kafa kwamitin binciken Sowore kan wasu makudan kudade
Source: UGC

KU KARANTA:Boko Haram ta kai harin da yayi sanadiyar rai guda da kuma batar mutum 6 a sansanin soji dake Gubio

A wani zance wanda ya fito daga majalisar zartarwa ta wannan jam’iya dauke da sanya hannun mukaddashin shugaban majalisar ta yi matukar nuna rashin jin dadinta akan kudi N157m da aka bayar gudumawa domin yakin neman zaben shugaban kasa amma sai dai anyi watanda da kudin.

Nzenwa yayi karin haske akan wannan lamari inda yake cewa, “ Duba ga badakkalar kudade da suka shafi magudi zaben da ya gabata a wasu jihohi mun kafa kwamiti domin binciken Mista Omoleye Sowore wanda shine shugaban jam’iyar AAC na kasa baki daya.

“ Ba mu dakatar da shi daga aikinsa ba, kwamiti ne mai kunshe da mutum uku wanda Hon. Musa Abu ke jagoranta zai bincike shi a cikin kwanaki bakwai daga nan sai mu san hukuncin da ya dace da shi, bayan mun samu cikakken rahoton abinda ya faru.” Inji Nzenwa.

Idan baku manta ba dai ana zargin Omoleye Sowore ne da karbar kudi $1m domin aikata zamba cikin aminci daga jam’iyun adawa.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

KU LATSA : Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel