Abinda yasa muke samun nasara a yaki da 'yan bindiga a Sokoto - Kwamandan sojoji

Abinda yasa muke samun nasara a yaki da 'yan bindiga a Sokoto - Kwamandan sojoji

Babban kwamandan rundunar soji ta 8 dake jihar Sokoto, Janar Hakeem Oladapo Otiki, ya ce hadin kai tsakanin rundunar soji da sauran hukumomin tsaro dake aiki a jihar ne sirrin nasarar da suke samu a yaki da 'yan bindiga da sauran kalubalen tsaro.

"Hada kan da muka yi wajen gudanar da atisayen hadin gwuiwa a jihar ya yi sanadiyar kama ,yan ta'adda da masu laifi 22 a tsakanin ranar 19 zuwa 21 ga watan Mayu. Masu laifin da muka kama sun hada da dillalan miyagun kwayoyi, 'yan fashi da makami, wadanda suka mallaki muggan makamai ba bisa ka'aida ba da sauran su," a cewar sa.

Wannan bayani na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mataimakin darektan hulda da jama'a na rundunar soji ta daya, Laftanal Ayobami Oni-Orisan.

Kwamandan sojojin ya bayar da tabbacin shirin rundunar da yake kagoranta na kakkabe duk wasu 'yan ta'adda da aiyukan ta'addanci a jihar Sokoto.

Abinda yasa muke samun nasara a yaki da 'yan bindiga a Sokoto - Kwamandan sojoji

Abinda yasa muke samun nasara a yaki da 'yan bindiga a Sokoto - Kwamandan sojoji
Source: UGC

Ya bukaci jama'a da suke gaggauta sanar da hukumomin tsaro duk wani abu ko yunkuri da kan iya zama barazana ga zaman lafiya a yankunan su domin daukan mataki ba tare da bata lokaci ba.

DUBA WANNAN: Hotunan kayan laifi da masu laifi da 'yan ta'adda da aka yi bajakoli a Maiduguri

A wani labarin na Legit.ng, kun ji cewar rundunar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Borno tayi bajakolin masu laifi da 'yan ta'adda fiye da 50 da ta kama tare da kayan laifi da makaman su a hedikwatar rundnar dake Maiduguri, babban birnin jihar Borno.

Masu laifin da aka yi bajakolin sun hada da 'yan fashi da makami, masu garkuwa da mutane, wadanda suka aikata laifin kisa da kuma dillalan miyagun kwayoyi da sauran kayan maye.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel