Jam’iyyar APC ta taya Fayemi murnar zama Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya

Jam’iyyar APC ta taya Fayemi murnar zama Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya

Kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta taya gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi murna, bisa lashe zaben shugabancin kungiyar gwamnonin Najeiya da yayi.

A wani jawabi daga kakakin jam’iyyar na kasa, Lanre Issa-Onilu, yace “zabar Fayemi domin ya jagoranci kungiyar gwamnonin Najeriya har zuwa 2021 ya kasance zabi nagari duba ga tarin kokari da Fayemi yayi da kuma kwarewarsa a lokacin da yake a matsayin minister, gwamna da dai sauran mukamai da ya rika.

“Tun daga lokacin da aka kafa kungiyar gwamnonin Najeriya, ta kasance mai tabbatar da ingancin damukardiyya tare da tabbatar da shugabanci mai tsari a kasar.

Jam’iyyar APC ta taya Fayemi murnar zama Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya

Jam’iyyar APC ta taya Fayemi murnar zama Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya
Source: Depositphotos

“Muna da tabbacin cewa kungiyar ta NGF a karkashin jagorancin Fayemi zata ci gaba da gudanar da kyawawan ayyuka da hadin kai da nuna goyon baya ga gwamnati wacce shugaban kasa Muhammadu Buhari ke jagoranta, wajen cimma burin akidar kawo chanji ga yan Najeriya, musamman a lokacin da kasar ke shirya ma shekaru hudu masu zuwa a karkashin wannan gwamnati.”

KU KARANTA KUMA: Rundunar yan sanda tayi umurnin kama direbobin mota masu bakin gilashi

Jam’iyyar ta yiwa Fayemi fatan alkhairi a gwamnatinsa kuma tana fatan ganin kyakyawar dangantaka tsakanin NGF da gwamnatin APC da shugaban kasa Muhammadu Buhari ke jagoranta.

Wannan babu shakka zai tabbatar da nasara wajen aiwatar da shirye shirye don cigaban kasar baki daya”.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel