An cafke wani limami da yake kokarin sace wani yaro dan shekara 11

An cafke wani limami da yake kokarin sace wani yaro dan shekara 11

- Jami'an hukumar 'yan sanda sun yi nasarar cafke wani limanin coci a lokacin da suke kokarin guduwa da wani yaro da suka sata mai shekaru 11 a wani kauye

- An cafke limamin shi da abokanan aikinsa a lokacin da suka sanya yaron a mota suke kokarin guduwa da shi

An samu nasarar cafke wani limamin coci dan shekaru 30 a duniya mai suna Samuel Emeka, wanda ake zargin ya sace wani yaro mai shekaru 11 a duniya a garin Awkuzu, a karamar hukumar Oyi dake jihar Anambra.

Wanda ake zargin, dan asalin garin Awkuzu, an bayyana cewa ya sace yaron mai suna Ikechukwu Ozoekwe a kauyen Umoubi shi da abokanansa.

Majiyarmu LEGIT.NG ta samu rahoton cewa barayin sun danna yaron cikin mota ta karfin tsiya, inda suka gudu dashi, sai dai kuma an kama su a lokacin da suke gudu da yaron a motar.

An cafke wani limami da yake kokarin sace wani yaro dan shekara 11

An cafke wani limami da yake kokarin sace wani yaro dan shekara 11
Source: Depositphotos

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar, Haruna Mohammed ya ce an kama faston tare da abokanan aikinsa.

Ya ce sun kwace yaron yanzu haka yana gurin mahaifiyarsa cikin koshin lafiya.

KU KARANTA: Bayan shafe shekaru 8 yana mulki, Al-Makura yana rokon zababben gwamna akan ya kara masa wa'adin wata 3

Ya ce, "A ranar 21 ga watan Mayu shekarar 2019 da misalin karfe 5:30 na yamma, jami'an 'yan sanda sunyi nasarar kama Fasto Nweke Chijioke mai shekaru 33 da kuma Samuel Emeka mai shekaru 30 duka a garin Awkuzu dake karamar hukumar Oyi jihar Anambra.

"Wadanda ake tuhumar, ana zargin sun sace wani yaro mai suna Ikechukwu Ozoekwe a ranar 18 ga watan Mayu shekarar 2019, da misalin karfe 4:30 na yamma a garin Akwuzu inda suka sanya shi cikin mota suka yi kokarin guduwa da shi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel