Buhari ya taya Gwamna Fayemi murnar zama shugaban gwamnonin Najeriya

Buhari ya taya Gwamna Fayemi murnar zama shugaban gwamnonin Najeriya

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Gwamna Kayode Fayemi na jihar Ekiti murnar zaman Shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya.

Shugaban kasar ya nuna yakinin cewa kowa yayi na’am wajen zabar Dr. Fayemi, cewa hakan ya nuna tarin karfin gwiwa da takwarorinsa ke dashi a kansa.

Ya bukaci sabon Shugaban da ya kalli zabensa a matsayin wani daman a musamman wajen wanzar da aminci da karfin gwiwar aiki tare da gwamnatin tarayya, da kuma sauran bangarorin gwamnati.

Buhari ya taya Gwamna Fayemi murnar zama shugaban gwamnonin Najeriya

Buhari ya taya Gwamna Fayemi murnar zama shugaban gwamnonin Najeriya
Source: Depositphotos

Buhari ya jadadda cewa “manufar kkungiyar gwamnonin Najeriya a koda yaushe shine sanya ra’ayin al’umman kasar nan sama da komai kama daga banbancin akida, siyasa , addini ko kabilanci.”

Shugaban kasar ya kuma nuna shirin gwamnatin tarayya na tallafa wa kungiyar wajen aiwatar da manufofinta.

Yayinda yake yiwa Fayemi fatan kammala shugabanci cikin nasara, Shugaban kasar ya yaba ma Shugaban kungiyar mai baring ado, Gwamna Abdul’aziz Yari na jihar Zamfara akan shugabancinsa a kungiyar.

KU KARANTA KUMA: Ayyukan yan bindiga: Daraktan Kannywood, Falalu Dorayi yayi kira ga yan arewa da su kare kansu

A baya Legit.ng ta rahoto cewa, kwamitin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ta taya gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi murna, bisa lashe zaben shugabancin kungiyar gwamnonin Najeiya da yayi.

A wani jawabi daga kakakin jam’iyyar na kasa, Lanre Issa-Onilu, yace “zabar Fayemi domin ya jagoranci kungiyar gwamnonin Najeriya har zuwa 2021 ya kasance zabi nagari duba ga tarin kokari da Fayemi yayi da kuma kwarewarsa a lokacin da yake a matsayin minister, gwamna da dai sauran mukamai da ya rika.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel