Dalilin da ya sa na maka Sufeton 'Yan sanda a kotu - Adeleke

Dalilin da ya sa na maka Sufeton 'Yan sanda a kotu - Adeleke

Dan takarar kujerar gwamnan jihar Osun a karkashin inuwa ta jam'iyyar PDP yayin zaben da aka gudanar a watan Satumba na shekarar 2018 da ta gabata, Sanata Ademola Adeleke, ya fayacce dalilin sa na maka sufeto janar na 'yan sanda a gaban kuliya.

Sanata Adeleke ya yi karar babban sufeton 'yan sanda a gaban kotu a sakamakon daduma tare da tsare shi a garin Abuja a ranar 6a ga watan Mayun 2019.

Tsohon Sanatan ya garzaya babbar kotun jihar Osun ta yankin Ikirun domin neman hakki a kan haramta masa 'yancin sa na walwala duka da shimfidar umurnin kotun bisa jagorancin Alkali Jide Falola akan kada hukumar 'yan sanda ta kusance shi.

Sanata Ademola Adeleke

Sanata Ademola Adeleke
Source: Depositphotos

Duk da takaddamar zargin sa da aikata laifi na zamba, kotun tun a baya bisa ga umurnin Alkali I.E Ekwor, ta ba Sanata Adeleke damar ficewa daga Najeriya a tsakanin ranar 7 ga watan Mayu zuwa 9 ga watan Yunin 2019 domin neman kulawa da lafiyar sa a kasar Amurka.

Sai dai hukumar 'yan sandan Najeriya ta yiwa umurnin kotun kunnen uwar shegu inda a ranar 6 ga watan Mayun 2019, ta nannade Sanata Adeleke tare da sakaya shi a sakamakon zargin sa da babban laifi na amfani da takardun shidar kammala karatun Sakandire na bogi.

KARANTA KUMA: ASUU ta yi barazanar koma wa yajin aiki a kan rashin cika alkawarin gwamnati

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, ana zargin Sanata Adeleke da gabatar da takardun shaidar kammala karatu na bogi yayin takarar kujerar Sanata a shekarar 2017 inda ya yi nasara akan dan takara na jam'iyyar APC, Sanata Mudashiru Hussein.

Yayin musanta wannan zargi, Sanata Adeleke cikin sabunta korafin sa a gaban kotu, ya yi karar sufeto janar na 'yan sanda, Muhammadu Adamu da kuma wasu manyan jami'ai, Simon Lough da John Faluyi.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid=solomonovlink

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta a Facebook ko kuma Twitter:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi:

https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel