PDP ta bukaci Lai Mohammed ya roke ta gafara

PDP ta bukaci Lai Mohammed ya roke ta gafara

- Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta bukaaci Ministan Labarai da Al'adu da ya fito yaa roketa gafara akan zargin da yayi mata na cewa ta na kokarin kawo cikas ga gwamnatin shugaba Buhari

- Jam'iyyar ta ce maganganun ministan ya nuna cewa suna kokarin ko ta wane hali sai sun batawa jam'iyyar PDP suna a idon al'umma

Babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta bukaci Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed da ya fito ya bata hakuri, bayan ya bata mata suna a idon al'ummar Najeriya.

Babbar jam'iyyar adawar ta ce ministan yayi mata kagen zata yi magudi a lokacin zaben shugaban kasa da aka gabatar ranar 23 ga watan Fabrairu.

A wata sanarwa da mai magana da yawun jam'iyyar Mista Kola Ologbondiyan ya fitar jiya Laraba a Abuja, ya ce magana biyun da ministan yayi ta nuna cewa shi da yake wakiltar gwamnatin tarayya babu abinda ya iya sai kage, inda yace jam'iyyar PDP da dan takarar ta Atiku Abubakar suna kokarin kawo cikas wurin rantsar da shugaban kasa Muhammadu Buhari.

PDP ta bukaci Lai Mohammed ya roke ta gafara

PDP ta bukaci Lai Mohammed ya roke ta gafara
Source: Depositphotos

Ya bayyana zarin ministan a matsayin alamu dake nuna cewa gwamnatin shugaba Buhari ta na so tabi ko ta wanne hali domin 'yan Najeriya su amince da ita.

Sanarwar ta kara da cewa: "Bugu da kari, ministan yace ya samo labarin nashi daga wata ma'aikata a kasar nan, sai dai kuma har yanzu ba wata ma'aikata ko hukuma da ta fito tana zargin PDP a matsayin ta na jam'iyya ko kuma dan takarar shugaban kasa a Atiku Abubakar a matsayin wadadan za su kawo cikas a gwamnatin Buhari.

KU KARANTA: A karon farko Sheikh Dahiru Bauchi yayi karin haske akan raba masarautun Kano

"Muna jin tsoron Alhaji Lai Mohammed yayi wannan ikirari ne saboda ya samu hanyar yiwa jam'iyyar PDP kage, ya kuma tursasa al'umma su fara ganin bakin jam'iyyar.

"Irin wannan maganar ba ta da amfani, tunda 'yan Najeriya sun riga sun gama gano su, kuma sun nuna cewa suna tare da Atiku Abubakar a kokarin da yake na kwato mulkin da aka yi mishi magudi a kotu.

"Saboda haka, jam'iyyar PDP tana bukatar Alhaji Lai Mohammed da ya fito ya bata hakuri, sannan ya bai wa 'yan Najeriya hakuri akan wannan labarin da ya kago da kanshi."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel